Kai!

 



Duk wanda ka ga ya gamu da mummunar kaddara, ko yana wata barna... ba abin dariya ba ne, abin tausayi ne.

Abin tambayar ma shi ne, taya  tawa kaddara zata kasance nan gaba? Shin ni na shiryar da kaina a yadda nake har nake jin ni mutumin kirki ne? Allah ne!

Babu wanda ya fi karfin gamuwa da mummunar kaddara, duk taka-tsantsan ko siffantuwa ta kamala; Allah na iya jarrabaka da jinya, hatsari, hauka, rashin imani, ko abin kunyar da makusantanka ma sai suna jin kunyar duniya... sai dai Allah Ya kiyaye.

Tsakaninka da mai barna, ko wanda ya shiga komar mummunar kaddara... ka masa nasiha (in akwai bukata), addu'a ko kuma ka tsuke bakinka. In bakinka babu alheri, gwamma ka yi shiru kurum. 

Sau da yawa Allah Ya fi jarraba mu da abin da bakunanmu suke furtawa kan wasu. Ka kuma lissafa, shin abin da kake kanana baka taba zagin wasu a baya akan su ba? Shugabanninmu misali ne na zahiri.

Kai dai ka yi addu'a Allah Ya mana tsari da mummunar kaddara (tragic end).


(c) Aliyu M. Ahmad

23rd J/Awwal, 1443AH

26th January, 2021.

Post a Comment

0 Comments