SABODA MUN FI TSORON KUNYAR DUNIYA...

 

Duk da ina jin nauyin maganar nan, amma SABODA MUN FI TSORON ABIN KUNYAR DUNIYA ne…

 

Na kan sha mamaki idan wasu iyayen, ko jama’a suka takurawa ‘ya mace akan maganar aure, amma ga 'da namiji ko oho!

 

Za ka sha mamaki a takurawa yarinya cewar sai ta fito da mijin aure, sai ka ce da ake siyowa a kasuwa, saboda gudun kar ta lalace; amma 'da namiji kuwa ko oho!

 

Ko kuma saboda ita mace nauyi ce (liability), shi kuma na miji kusan shi ke daukar nauyin rayuwarsa? Eh, darajar mace a cikin kowacce al’umma da addini, shi ne ta zauna a gidan mijinta, wannan ba bu ja! Amma fa (wani) na mijin za a aurar da kannensa mata 3, 5, ... ba a damu a rufa masa asiri ba, don ya kare kansa daga afkawa barna.

 

Amma kuma za ku yarda da ni in na ce, “mun fi gudun ABIN KUNYAR DUNIYA AKAN NA LAHIRA?” Ma’ana saboda ita ‘ya mace, za ta yi cikin sh*ge, in ta bi sawu, kuma za a sani, labarin lalacewarta zai shiga cikin dangi (family) da gari (community) ya batawa gidansu suna, ya sa iyayenta kunyar duniya, shi ya sa ake gudun wannan abin kunya? Amma ga namiji kuma, an manta da girman sabo da kuma girman wanda ake sabawa (Allah).

 

Misali, ta iyu, wata 'kilakin' ta shafe shekara-da-shekaru tana ta’asarta, ba tare da taba cikin sh*ge ba, saboda kwarewa da kuma amfani da wasu kwayoyi na hana shigar ciki; amma wata sabuwar shiga, a taku daya, in da tsautsayi sai ka ga ta kara nauyi.

 

Na kan tambayi kaina, idan yarinya ta tashi lalacewa, waye abokin lalacewar ta ta? Na miji? Ba a damuwa da shi, saboda shi ba ya ciki ko? Amma sabon fa?

 

Mun fi runtse ido akan bin kunyar duniya, fiye da sabo, da kuma rashin duba girman Wanda ake sabawa. Ba mu tuna ranar da za a zo a yi mana tutsiye a ranar Hisabi (Alkiyama).

 

Sabon zina ga namiji ko mace duk daya ne; bambancin kawai a tsarin halitta ne; mace na daukar ciki, namiji kuma baya daukar ciki. Da ciki ko ba ciki, laifin zina, zina ce; kuma laifi ne, sabo ne babba. Shi ya sa ko a wajen haddi, Alkur'ani Maigirma, cikin Nur, aya ta 2 aka ce; "الزانية والزانى.." duk jinsi biyun aka ambata.

 

Hakika! Hakki ne akan iyaye, kare dukkan ‘ya’yan daga afkawa sabo, mace ko namiji, musamman a wannan zamani da tarbiyya ta zama abin da ta zama. Kuma, wajibi ne akan iyaye bawa 'ya'ya tarbiyya da ilimi don tseratar da kansu da kuma 'ya'yan (mata da maza) daga uƙubar Ubangiji (Tahrim: 6).

 

(c) Aliyu M. Ahmad

3rd Jumada II, 1443AH

7th January, 2022CE

Post a Comment

0 Comments