A DA CAN ƊA NAKOWA NE...

Ko mu ƴan 1990s, mun shaida yadda iyayenmu suka maida mu ɗaya da ƴaƴan makwafta. Sukan mana abubuwa a yarintarmu tare ba bambanci, shayi (kaciya), ɗinkin sallah, tsawatarwa, aika da sauransu.

Amma a yau, ko tsawatarwa yaro ka yi in yana shaƙiyanci a layi/titi ko kai ƙorafinsa ga magabatansa, sai ka zama kai ne mai laifi. A yau ka ce zaka yi gwanintar haɗa ƴaƴanka da ƴaƴan makwafta shayi/kaciya, ko sa su a makaranta ko wata Islamiyya sai ranka ya ɓaci.

Gudun  ɓacin rai yasa al'ummarmu a yau tsuke baki (shiru) in sun ga yaro ko yarinya suna ba daidai ba har sai in abin ya bayyana ƙarara ga magabatan nasu, wanda hakan kuskure ne da muka samu kanmu a yau. Yaro zai fara shaye-shaye ko yarinya zata fara yawace-yawace, har sai sun zama addicted/sun yi nisa tukun iyayen za su sani.

Haka A DA in ka mutu baka da shakkun masu riƙe maka ƴaƴa saboda zumunci. Amma a yau in ka ga ana rububin ɗaukar ƴaƴa bayan mutuwar uban, tabbata ya bar wani abu ne na gado mai ƙauri; in ba haka ba kuma, sai dai mahaifiyarsu ta yi ta wahala da su. Wannan ke tilasta ɗorawa yara Talla, da nisanta su da neman ilimi.

A da in ka ji ana cewa ƊA NA KOWA NE, tabbas hakan ake nufi. Amma a yau kam, sai in yaro ya yi gwagwarmayar rayuwa, Allah Ya masa nasibi da samun madafar iko, dukiya ko shuhura yana da MAMORA a nan yake zama na kowa, don za a more shi. In ba haka ba kuwa, ƊA NA IYA MAI SHI NE.

Nuna halin ko'in kula yanke zumunci ne cikin al'umma, kuskure ne babba, kuma da sannu hakan zai farauce mu matuƙar ba mu yi kokarin gyarawa ba.

(c) Aliyu M. Ahmad

06041442AH 21112020CE


Photo Credit:  Mike Blyth | Flickr

Post a Comment

0 Comments