SABUWAR SHEKARA

 

Shi wani yana ƙorafin bai yi aure ko samun cikar wani burinsa ba a 2020/2021 har ta wuce. Shi ko wani ko ƙarshen 2020/2021 ma bai zo da numfashi ba (ya mutu). Wani kuwa yana kwance jinya a asibiti ko cikin gida, duk ba don sun yiwa Ubangiji laifi ba.

In muka yi tunani ma, akwai ɗaruruwa suna rayuwa a ƙuntace cikin magarƙama (prison), ba tare da sun san laifin da suka aikata ba. Kai ko kana zaune cikin rufin asiri, ba ‘pending’ sauraro daga Kotu, Ofishin Hisbah ko na ƴan sanda.

Kai! Matuƙar kana numfasawa, lalle Ubangiji ya ma ni'ima ta rai da rayuwa. Matuƙar kana iya taka ƙasa da ƙafafunka, lalle alama ce tana kana cikin masu lafiya. Matuƙar kana zaune ba yunwa, lalle alama ce ta kana cikin ƙosasshu… amma kasan adadin da yunwa ta kashe a iya yau ma?

Eh! Duk da 2020/2021 shekara ce mai tattare da ƙalubale na matsin rayuwa da tattali, fargaba, rashe-rashe, kashe-kashe; amma har yanzu NI da KAI mai karanta wannan rubutu muna cikin rayayyu, Alhmadulillah!

Sabuwar shekara ba wai sauyi ba ce, kalubale ce a kaina da kai, domin mu auna abubuwa da kuka kasa yi a tsohuwar shekarar shin ko za mu iya yi a sabuwar shekara mai zuwa? Kai zaka bawa kanka wannan amsar. Domin Allah ya sanya jujjuyawar rana da wata domin zuwa aya ga masu tunani, tsoron Allah, hankali da kuma mu san lissafin kwanaki [Al-Isra’ aya ta 12; dss].

Sabuwar shekara bata nufin sabon sauyi, a'a, ita ma rana ce kamar sauran ranaku da kake rayuwa. Inda kuwa kana buƙatar ganin sauyi, ko cikar wani buri, sai fa ka yi huɓɓasa da gasken gaske... tare da haɗawa da sinadaran jajircewa, haƙuri, addu'a da neman shawarwari.

Idan ma ka rasa wani abu jiya, ka tuna Mai bayarwa (Allah) Yana bayarwa tun kafin a halicceka, zai kuma ci gaba da bawa bayinsa har bayan ranka. Ka kasance cikin masu godiya da tawakkali a kodayaushe, Allah ne zai baka daga falalarsa.

Tsakaninmu da Allah sai godiya, Allah Ya ƙara mana lafiya, ni'ima, rufin asiri, da zaman lafiya, ya kuma ba ku kariya daga dukkan sharri, amin.

* Tsohon rubutu ne na 2020.

 

(c) Aliyu M. Ahmad

16th J/Awwal, 1443AH 

Thurs. 31st December, 2021

Post a Comment

0 Comments