MATASA! MU SAKE TUNANI

 

Idan har yanzu kana tunanin, wai sai ka tara kudi ne, ko ka rike wata madafar iko tukun zaka iya taimakawa al'ummarka, yankinka ko na kasa da kai, hakika kana da tsukekken tunani... ka sake tunani, ka farka daga baccin da kake.

Allah Ya yi mutane daban-daban, tare da basu baiwa daban-daban, kamar yadda ya halicci gabban jikinka. Ya yi ma ido, don ya taimaka ma wajen gani, harshe da sauran gabbai don furuci, kafa don tafiya, hannu don tabawa ko dauka, hanci don sansane da numfashi, kunne don ji... idan ka hada wadannan gabban, sune suka taru suka samar da siffa ta mutum, kamil.

Kamar wadancan gabban, haka ma mutane suke, a matsayin al'umma guda, wannan ya rike can, wancan ya tallafa da can. Wani da iliminsa, wani hikima da baiwa, wani kuma da karfinsa, wani da kudi... amma duk mun fi barwa masu kudi da madafun iko dama.

Kamar yadda ya zo a wani hadisi na Abu Dharr رضي الله عنه, wata rana wasu Sahabbai رضوان الله عليهم suka zo wajen Annabi suna cewa, "Masu dukiya sun tafi da lada, domin suna sallah da azumi kamar yadda muke, kuma suna sadaka da mafi girma na dukiyoyinsu (da mu bamu da su), sai Manzon Allah Ya ke tambayarsu, "أو ليس قد جعل اللهً لكم ما تصدقون" "Shin kuma Allah bai sanya muku wani abu da zaku iya sadaka da shi ba?"  "...Umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummuna ma sadaka ce" [Muslim, 1006].

Yana daga cikin umarni da kyakkawan aiki, ilmantar da al'umma, domin da ilimi ne ake sani abin da ya dace da wanin haka kamar yadda Al-‘Allaama Al-Safarini AlHanbali رحمه الله ya fadi a cikin غذاء الألباب. Yana daga cikin umarni da kyakkyawa, da kuma hani da mummuna, tallafawa al’umma don zama mutanen kirki, da kuma nisantar kawo musu abubuwa da za su gurbata musu tarbiyya.

Allah ya sakawa Dr. Muhammad Mukhtar Aliyu da alherin duniya da lahira. Asali abin da malamanmu suke gaya mana shi ne, tun a karatu na gaba da sikandire; a Kwaleji, Poly, ko Jami'a ake kokarin bawa kowa horo, ta yadda mutum zai iya lalubo matsaloli a inda yake, ya yi bincike, ya lalumo sanadi na sanuwar matsalar, ya kuma nemo hanyoyin magance su, a wani aiki sa ake kira 'PROJECT' a mataki na kasa. Ba kuma ana yin wannan aikin ba ne, don samun maki (grade) kawai, a'a; ana son a dasa ma wannan tunani ne, har tsawon rayuwarka. Wannan shi ne babban bambanci tsakanin wanda ya je makaranta, da wanda bai je ba.

Idan yaran yankinku suna faduwa jarabawar English da Math, ko akwai karanci karatun addini, mene ne amfani karatun da kai ka yi da ba zaka tallafawa al'ummarka da shi ba? Ka yi karatun fasahar zamani, amma kana gani ana damfarar 'yan uwanka da wannan fasahar ️ Ka yi karatun lafiya ko na muhalli, amma unguwarku duk kazanta, ba zaku iya nusar da al'ummar illar kazanta ba? Ko sai NGOs sun kawo program da za a sami kudi? Ko sai ka sami madafa a siyasa? Ohhhh! Aikin kudi zaka yi kenan ba tallafawa al'umma ba 🙄🙄 Ko dai karatun kwali ne kawai 🤔🤔

Ka yi tunani, ba sai da iya kudi zaka kawowa yankinka ci gaba ko sauyi ba. Ka yi amfani da iya abin da ke hannunka. Tunani mai zurfi, bada shawarar mai kyau, sa ido da nusarwa, kauracewa zaman banza, zama mutumin kirki, kauracewa cutar da mutane ko bata musu tarbiyya... duk hanyoyi ne na kawo yankinka ci gaba.

Kullum ka tashi da tunanin, ta ya zaka tallafawa al'umma, kai ma sai Allah Ya tallafa maka daga falolinsa ta yadda baka tsammani.

 

(c) Aliyu M. Ahmad

3rd Rabi'ul Awwal, 1443AH

10th October, 2021




Post a Comment

0 Comments