GAYU A JI TSORON ALLAH

 


Wallahi! Ba karamin azzalumi ba ne kai... gaye!

Ka san ba aure za ka yi ba, baka da halin aure a yanzu, amma ka bi ka mallaki zuciyar 'yar mutane, har a kai ga matakin da za ta iya bijirewa umarnin iyayenta saboda ta faranta maka.

Wallahi matasa mu ji tsoron Allah, ba cinyewa ba ne wai ai an ce ana masifar sonka da gaskiya, kana hura hanci sama; alhalin kana jawa 'yar mutane la'anar Allah a kullum, ka tusawa iyayenta haushinta, ka kore masu kaunarta da gaske da aure, ka hada ta fada 'yan uwanta da masu gaya mata gaskiya... kaddara 'yarka ce ko kanwarka... ya zaka ji a ranka?

Dan gaye! Idan kana son kanka da lafiya, duniya da lahira, kar ka jefa ƙafarka, kar ka furtawa 'yar mutane kalaman karya da gaskiya da sunan so, in ka san baka shirya ba. In babu hali, Alqur'ani ya fada, sai a ci gaba da hakuri, حتى يغنيهم الله من فضله (Annur, aya ta 33).

Kai! Zalunci ne, in ka furta kalmar so, ga wanda ka san ba zaka iya cika alƙawarin son ba (aure), ka kuma sa ta bijerewa ko juyawa wadanda suka zo auranta da gaske baya, saboda son zuciyarka. Baka tsoron a lahira a tashe ka sahun makaryata, maciya amana, masu taimakawa aikin sabo (bijirewa iyaye)...

Wani labarin in ka ji, sai ka yi hawaye...

Iyaye kuma a rika bawa 'ya'ya darasi game da zaman duniya, da basu lokaci don saurarar abin dake ransu, don rayuwar 'da aka yi a baya' da 'wacce ake a yanzu' akwai bambanci mai tarin yawa sosai, yara na wayewa da sanin duniya fiye da tunani, sai an dage sosai wajen sa ido, tarbiyya, addu'a da jan 'ya'ya a jiki, ba sai abu ya lalace ba ana da-na-sani.

Mu ji tsoron Allah.
Allah Ya shirye mu ya shirya mana zuri'a.

(c) Aliyu M. Ahmad
4th Rabi'ul Awwal, 1443AH
11th October, 2021CE

Post a Comment

0 Comments