KA YI TUNANI, DON AN BAR MA ABUBUWAN TUNANI...



Yi tunani, don an bar ma abubuwan tunani masu yawa.

Iya FACEBOOK, WHATSAPP and INSTA aka janye na ɗan lokaci, ka ga yadda hankula suka tashi?

Waɗannan manhajojin (apps), ko da su, ko babu su zaka iya rayuwa, kuma cikin ƙanƙanin lokaci za ka iya warkewa daga wawan sabon (addiction) da ka musu. 

Ina ga ace ni'imar ruwan sha, ko lafiya, ko gani, ko ji, ko kwanciyar hankali aka ɗauke ma fa? Ina ga a ce kana cikin kabari (القبر) ne, inda ba wata a ba, social media; ba ka da access da internet, ba lantarki, ba... daga kai sai aiyukanka?

Na biyu, yadda waɗannan manhajoji (apps) suka ɗauke farat ɗaya (ba tare da mun san hakan zata kasance ba), har muka shiga juyayi; haka mutuwa za ta zo mana, farat ɗaya, ba tare da ta sanar da mu ba 😰

Na uku, daga samun matsalar manhajojin Mark Zuckerberg (FIW), a yammaci Lahadi (jiya 4th October, 2021) zuwa ƙarfe 10:40pm (na daren jiya), an samu ƙaruwar sauƙe manhajar 'Telegram' da yawa, wacce take a madadin Whatsapp, hakanan, an samu ƙaruwar amfani da VPN don buɗe Twitter, ga ƴan Nijeriya (Bloomberg, 2021).

Christopher Walken (1943 -) yake cewa: "Da mutane sun san yadda ake mantawa da su bayan mutuwarsu, da sun daina rayuwa don burge mutane." Wallahi! Da zarar ka bar duniya, ko ka rasa wani abun duniya ko wata dama, cikin ƙanƙanin lokaci mutane za su juya ma baya, su manta da samuwarka, su koma inda buƙatarsu za ta biya. 

Ka bi Allah, ka huta.
Ka yi don Allah, ka rabauta.

(c) Aliyu M. Ahmad 
27th Safar, 1443AH
5th October, 2021

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Facebook #Whatsapp #Instagram #Outrage

Post a Comment

1 Comments