ZAMA DA DATTAWA



Wata falala daga cikin zama da dattijai, za su karantar da kai darasin rayuwa ne a yadda take a zahiri, kasancewar sun rayu shekara-da-shekaru, sun yi gwargwamaya, sun san tashi da faɗin rayuwa, sun kuma yi mu’amala da mutane daban-daban. Dattawa sun san waye mutum! Hausawa suka ce “da na gaba, ake gane zurfin ruwa.”

Fitata yau da yamma dan yawon Juma'a, na zauna da wani dattijo, kamar wasa sai na tambaye shi da ya koya min wani darasi game da rayuwa, a matsayinsa na wanda ya manyanta. 

Wasu daga cikin darussa da ya karantar da ni, su ne; ya ce:

1. Ba zaka taɓa zama wani abu ba a rayuwa, har sai ka yi wani abu. Darajarka a idon mutane, gwargwadon amfanarka da suke ne. A yau in ba a amfanarka, kai ba kowa ba ne, babu wanda ya damu da kai. Ka kula da kanka, ka kuma amfanar da waɗanda suke kusa da kai, DON ALLAH. 

2. A matsayinka na matashi, gina kai, shi ne ya kamaceka, kar ka biyewa ƙuruciya;

• Ka nemi kuɗi, 
• Ka nemi ilimi, 
• Ka riƙe mutuncika. 

A yau, ko kai ne ɗan autan gidanku, IN KA FI KOWA KUƊI (a gidan), KAI NE BABBA.

Kar ka yi gaggawa, don mallaka wani abu, ko zama wani; don ‘ba’a shan zuma sai an sha harbi.’

Kar ka raina kowa, don ‘kowanne mutum da rana tasa.’

Kar ka yi gasa da kowa, balle har ka masa hassada; 

Kowa da ka gani, akwai baiwar da Allah Ya masa, sai dai mutane da yawa suna rasa sanin ta su baiwar ne, saboda suna hange ta wasu. 

3. Kar ka taɓa tsammanin wani ɗan Adam zai ma wani abu a matsayin sakayyar alherin da ka ke masa. Don ka yiwa wani abun kirki, kar ka sa tsammani zai saka ma da alheri, kai dai kawai ka yi masa DON ALLAH. Wani lokacin, waɗanda kake taimaka sune suke baka matsala a rayuwa. Wasu baren ma, sun fi wasu ƴan uwa na jini. 

Ka kiyayi mutum, kamar yadda aka baka ‘Falaqi’ da ‘Nassi’ (ma’ana, ka nemi tsarin Allah daga sharrin mutum).

4. Kar ka kuskura ka yi aure, ba tare da ka shirya ba. Ina mai tabbatar ma, yin aure cikin kunci, tarko ne na talauci, har mutuwa, sai wanda Allah ceta. Kar ka biyewa ƙuruciya, da gasa da abokai, aure shi ne madubin rayuwar da ta rage ma a duniya. Komai zurfin sonka ga mutum, kar ka auri wanda baya ƙaunarka.

5. In ka tashi aure, ka duba mace wacce kake son ‘ya‘yanka su yi koyi da ita. In kana son ‘ya’yan masu tarbiyya da ilimi, sai ka nemi mace mai irin waɗannan siffofin. Kyau, yana tsufa, halayya kuma, da ita ake zama a gidan aure. Ka sani: "Macijiya bata haifar akuya, sai dai ta haifi macijiya ‘yar uwarta."

Haƙiƙa! A wurin dattawa akwai ilimin rayuwa mai tarin yawa da matasa za su kwasa matuƙar sun kusance su (amma ba a gurin kowanne irin dattijo ba, don akwai nagari, mai hikima, mai ilimi da kuma wanin haka).

Ka ziyarci dattawa a unguwa ko na cikin dangi (family), dattawan malamai a addini ko boko, ko dattawan ƴan siyasa, ko ƴan kasuwa, ma'aikata dss. don ka kwashi ilimai a araha, (kuma) cikin raha. Daga baya ka gode min.

Allah Ya karawa manyanu albarka da lafiya. 

© Aliyu M. Ahmad
2nd Safar, 1443AH
10th October, 2021CE

Post a Comment

0 Comments