CIWON HAUKA/CUTAR KWAKWALWA


Ciwon hauka kamar sauran cututtuka irin su Malaria, Typhoid, Ulcer dss, yana iya kama kowane mutum. Hakanan, kamar ciwon wasu sassan jiki: ciwon kunne, ido, haÆ™ori, sanyin Æ™ashi/kafa dss ita ma kwakwalwa kan iya shiga É—an ruÉ—u na ‘yan wasu lokuta. 

Ba kuma sai lalle sai mutum yana yawo cikin Æ™azanta ko surutai barkatai ba ne yake da cutar kwakwalwa, da yawan cututtukan kwakwalwa suna bayyana ne a cikin halayyarmu da mu’amalarmu ta yau da kullum (mis. personality disorder), kuma É—aiÉ—aikun mutane ne suka tsira daga wasu dangogin cututtukan kwakwalwa. 

Wasu daga cikin cututtukan kwakwalwa na samun wasu mutanen ne saboda wasu abubuwa da suka same su a baya na tsoro (mis. Phobias), cin amana (mis. Pistanthrophobia), rasa wata dama ko wani/mutum (mis. PTSD) kowa ya danganta da nasa [Rachman, 1978], kuma suna da matuÆ™ar tasiri a mu’amalar mutum, kamar sa yawan tsoro, kaÉ—aici, tsoron mace/namiji, yawan fushi, mahaukacin son kudi, Æ™in shiga cikin mutane, yawan mantuwa, shaye-shaye dss wasu tun daga yarinta. 

Shi ya sa, kafin ka yi mu’amala da wasu mutane ko aure, yana da kyau ka san lafiyar kwakwalwarsu. Kuma hira da ake tsakanin saurayi da budurwa, dama ce ga masu niyyar aure da ya kamata su fahimci junansu; amma abin haushi sai an shiga gida ne ake wannan Æ™oÆ™arin, daga Æ™arshe sai ka ga auren baya jimawa.   

Wasu daga cikin cututtukan haukan suna buÆ™atar ganin likitan kwakwalwa da yanayin halayya (Psychotherapist) [Jeffrey 2004], wasu kuwa na buÆ™atar nuna kulawa daga ‘yan uwa (rarrashi, ta’aziyya, jaje dss) ko magunguna da suka danganci wannan matsalar [Stahl, 2008]. Amma mafi Æ™ololuwar abin da mutum zai lazimci yi don sauÆ™aÆ™awa kansa sarrafa kwakwalwa/tunani shi ne lazimtar Zikiri (Karatun Alkur’ani, Istigfari, Salatin Annabi (S.A.W.), dss) [Ar-Ra‘d 13:28]  

© Aliyu M. Ahmad
05051442AH 21122020CE

Post a Comment

0 Comments