DA MA TSAKANINA DA KU KENAN 🤔?


Yanzu duk soyayyar da ke tsakanina da ku, idan na MUTU, rami zaku haƙa ku binne ni cikin ƙasa? 

Ga matsi, babu sarari; 
Ga duhu, babu ko ƴar ɓula
Ko hasken rana da wata (cikin dare) ba za su shigo kabarina ba.

Abokaina, ƴan uwana, har da ku a kwaɓa ƙasar da za a binne ni? 😢 Au! Wasu ƴan uwana ne ma na jini, da masoyana, za su kama gawata su saka a rami.

A lokacin da kuke binne ni, har ji nake wani na faɗin: "ga wata yar ƙofa can, ku sa ƙasa da ganyen maina, ku toshe." 

Wani kuma can a gefe, cewa yake: "ramin ya yiwa gawar faɗi, sai an rage, ta yadda gawar ba za ta yi motsi ba..."

Duk abin da na tara, dangina, ku zan barwa ku gaje shi, ni kuma na je can, na fara amsa 'query', a ina na sami kuɗaɗen? Ta yaya na tara dukiya? Wanɗanda na kashe kafin na mutu, a ina na ɓatar da su?

Ba wannan ba, sai an tambaye ni, me na yi a duk cikin sakanni 86400 (daƙiƙa 1440/awa 24) na kowacce rana. Abin kirki nake, ko na tsiya?

Yanzu in na mutu, ba wata sauran alaƙa tsakanina da ku, ba wata hulɗar kasuwanci, babu ta auratayya. Da yawan ku ma, sai kun manta da na taɓa rayuwa a duniyar nan. Duk soyayyar dake tsakanina da budurwata, wani saurayin zata sake; matata, wani mijin za ta je ta aura, ƴaƴana, dukiyata za su rabe a matsayin gado...

Haka ne tsakanina da ku?

Kuma fa hakan shi ne gatan, da ka mutu a ma sutura ta mutunci, a raka har gidanka na gaskiya (kabari).

Tsakanina da ku, a iya nan duniya ne, in da wanda ya taɓa ɓatawa, ya yafe ni, in kun ji labarin mutuwata, ku min addu'a, ku nema min gafara.
 
Idan har kana cikin masu tunawa da wannan waƙi'ar mai zuwa, don me zaka tsaya burge abin halitta, ka manta da Mahalicci; ka tara dukiya (ta ƙazamar hanya) wasu za su ci gado, amma hisabi na kanka. Ka ƙi tsaida sallah, ka yi zalunci, a je inda ake shari'a, ba lauya, babu karɓar kwaranshin (cin hanci). An kuwa a cikin mu'amalarmu, da neman duniyarmu a yau, muna tuna cewa za mu mutu kuwa?

Christopher Walken yake cewa: "Da mutum ya san yadda mutane suke mantawa da samuwarsa bayan ya mutu, da ya daina rayuwa don ya burge kowa." Ka rayu don ka burge wanda ya yi ka da manufa (ta ka bauta masa). "Ku gayawa duk wanda mutuwa ba ta zame masa wa'azi ba, ba ni, ba shi" in ji Manzon Allah ﷺ.

Allah Ya sa mu cika da imani.

(c) Aliyu M. Ahmad
5th Safar, 1443AH
13th September, 2021CE


Post a Comment

0 Comments