TA YAYA ZAN KWARE WAJEN SARRAFA COMPUTER?


Wannan ita ce tambayar da nake samu akai-akai daga abokaina na Facebook, makaranta da kuma abokan hulɗa na kasuwanci, na (kuma) ga ya kamata na ɗan kaɗa tawada (yau) bisanta.

To! Kasancewar muna rayuwa a cikin Ƙarni na 21 (21st century), ƙarnin da ake yiwa ƙirari da ‘information age’, ‘computer age’, ‘digital age’, ‘new media age’ da sauransu, dole ne wanda yake rayuwa a wannan ƙarnin ya tafi da zamani, ta hanyar iya amfani da na’ura mai kwakwalwa (computer), tare da kula da duk wani shige da fice na bayanai a yanar gizo-gizo (internet). 

Rashin saka ƙafa wajen mu’amala da sabbin fasahohin zamani, ko iya amfani da na’ura mai kwakwalwa, zai sa a riƙa yin abubuwa ana barinka a baya sosai. Babban misali, rashin sanin ilimin yadda za a sarrafa ‘computer’ yana daga cikin dalilan faɗuwar ɗalibai jarabawar JAMB (CB) kamar yadda masu bincike suka fitar (Oyeniyi, 2020).

Insha Allahu! Idan kana son ka kware sosai wajen sanin yadda zaka iya sarrafa ‘computer’, waɗannan matakan za su iya taimaka ma sosai:

Matakin farko: Mallakar kwamfuta

Matuƙar kana son ka iya ‘computer’ sosai, yana kyau ace taka ce, ta kanka; ba ta aro ba, kar kuma ka dogara da ta iya ‘computer centre’ (inda ake koyar da ‘computer’) kaɗai. Dalili, a matsayinka na mai koyo, zaka fi yin amfani tare da maimaita abin da koya da ita, hankalinka kwance, a duk lokacin da kake so.

Mataki na biyu: Koya daga kwararre

Ka nemi wanda zai rika nuna ma abubuwa (malami), ka’ida ce ta koyon kowanne ilimi danganta koyonsa wajen wanda ya san fannin sosai, ko ziyarta makarantun koyar da 'computer'.
 
Mataki na uku: Naci (Earnest)

Ba zaka taɓa zama gwani ba a kowanne fanni, har sai ka sanya naci sosai. Abubuwa da yawa cikin computer na sauƙin koya, zaka iya koyarsu cikin ‘yan daƙiƙu, amma sai ka sa naci wajen tambayar a koya ma, kuma ka sa naci wajen son koyo ɗin. Hakanan, duk abin da aka koya ma, in kana son ya zauna a kanka sosai, dole sai ka riƙa maimaitawa akai-akai.
 
Matakin na huɗu: 

Sauran abubuwa da za su taimaka ma sosai wajen kwarewa wajen sarrafa ‘computer’ su ne; bibiyar darusan koyon ‘computer’ na ‘yan daƙiƙu a Youtube da karanta littafan koyon kwamfuta, wannan hanya ce mai muhimmaci sosai, har ga wanda ya kware ɗin ma, domin sanin/koyon sabbin hanyoyi da dabaru na sarrafa ‘computer’, tare da sanin hanyoyin sauƙaƙawa, kamar ‘shortcut keys.’

Mu kula! 

A matsayinka na mai koyon ‘computer’ a makatin farko, ka yi sani, ‘computer’ na da packages (manhajoji) da dama, sai ka fara koyo da mafi sauƙi, kamar wanda aka fi amfani da shi yau da gobe. Misali, akwai na wanda ake aiyukan adana bayanai (desktop publishing) kamar Microsoft Office package (Word, Excel, Power Point, Access, InfoPath…) da SPP, akwai na zane-zane (graphic) ko sarrafa hotuna masu motsi (motion pictures), kamar Adobe CS (Photoshop, Illustrator, After Effect, Lightroom…), CorelDraw, Canva, Pixlr… akwai na haɗa sabbin mahajoji (developers’ app), web devs da browsers, manhajojin na da yawa, ba su lissafu ba.   

Amfani da ‘desktop publishing packages’ zai sa ka zama ‘typist’ ko ‘desktop publisher’, ‘statistician’ ta amfani da ‘charts’ (bayani cikin hoto). Hakanan, da amfani da Adobe CS ko CorelDraw zaka iya zama ‘graphic designer.’ Zaka iya ‘web page’ idan kana da ra’ayin koyon Wix ko Dreamweaver, ko sauran ‘app devs’ na kirkiro manhajoji, wasanni (games) da sauransu.

Maganar gaskiya, yau da gobe ke sa a zama gwani, matuƙar ka nace, kuma ka samu mai saka ka a hanya, zaka kware cikin ƙanƙanin lokaci. 

© Aliyu M. Ahmad
5th Safar, 1443AH
13th September, 2021CE

* Photo Credit: Rotimi Popoola

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Hausa #Computer

Post a Comment

0 Comments