Iyaye! Don Allah ku riƙa sa 'ya'yanku a makarantun koyon Addini tun suna ƙanana, domin (wallahi) in sun girma nauye-nauyen rayuwa ba zai bar su su kai kansu (don su) koyo ba. Kuma, wajibi ne a kanku (iyaye) basu tarbiyya da ilimi don tseratar da kanku da su daga uƙubar Ubangiji (Tahrim: 6).
Karatun sanin Addini da yadda za a yi bauta da mu'amala cikin ilimi, shi ne karatun wajibi da Addini ya 'wajabta' a kan kowa. Ba gatan da zaka yiwa yaro/yarinya irin su sami ilimin sanin abin da zai kusanta su zuwa ga rahamar Allah, ya kuma nisantar da su daga shiga uƙubarSa.
Karatun addini na kaifafa kwakwalwar yaro, ta ginu, ya iya tunanin abu mai kyau da kaucewa mummuna. A karatun addini yaro ke sanin yiwa iyaye biyayya dole ne, saɓa musu bala'i ne. Sata haramun ce, neman halal wajibi ne. Zumunci dole ne. Yin gaskiya dole ne; kuma, ƙarya, ha'inci, yaudara, zamba da cin amana haramun ne. Tsafta dole ce, ƙazanta abar kyama ce. Ci da shan abubuwa masu kyauta da gina jiki falala ne, ta'amulli da miyagun kwayoyi da duk abu mai sa maye haramun ne. Auren abin so ne, zina, luwaɗi da maɗigo haramun ne. Haramun ne baiyana tsiraici ko sanya mummunar sutura. Cikin karatun addini ƴaƴanka za su san falalar haƙuri, juriya, kunya, tausayin halitta (humanity), da kuma sanin haramcin girman kai, raina mutane da kasala.
Wacce tarbiyya ce wacce ta fi wannan?
Wacce wahala zaka sha wajen tarbiyyar ƴaƴanka in sun san da wannan?
Kuma tabbas! Idan yaronka ya sami Alkur'ani (cikin ƙirjinsa), tamkar ka bashi makulli buɗe taskokin ilimi ne.
(c) Aliyu M. Ahmad
7th Safar, 1443AH
15th September, 2021
0 Comments