SHAZAM
Wani lokacin, in ka shiga motar haya, adaidaita sahu, ko ka kunna radiyo, ko ka shiga shagon aski/gidan kitso, ko na biki, ko restaurant, ka kan ji sautin Qira’ar Alqur’ani ta wani malami, ko wani sauti (na wakƙ), ka ji ranka yana so, bayan ka bar wajen kuma, sai ka yi ta tunanin, a ina zaka sami sunan mai wannan qira’ar, ko waƙar, ko mawaƙin.
To ga amsa, ka nemi SHAZAM.
Manhajar ‘Shazam’ wani ‘app’ ne na musamma da aka ƙirƙira dake iya lalubo sauti cikin ƙanƙanin lokaci (recognizer). Asali, wasu mutane 4 ne suka ƙirƙiri wannan manhajar a shekarar 1999 a London, daga baya, a 2018 kamfanin Apple Inc suka siye shi. A da, ana ƙiransa da ‘2580’, saboda sune lambobin da ake ƙira a ƙasashen Turai, don bawa mutum bayanai na wata waƙa, da sunan mawaƙi. An kuma fara ɗora ‘app’ ɗin da sunan ‘Shazam’ a manhajojin AppStore, Playstore da sauran rumbuna (database) a shekarar 2008. Kuma yana daga cikin top-100 apps a duniya (DigitalTrends, 2021).
An canja masa suna daga ‘2580’ zuwa ‘Shazam’ ne, sunan wani jarumin comic, Shazam (Captain Marvel, 1940). Wilford Fawceet (1885 - 1940) ya sanyawa ɗan wasansa (character/comic) Captain Marvel suna ‘Shazam’, daga harufan farko na sunayen wasu manyan jarumai 6 a tarihin duniya; Solomon (S, ‘hikima’), Hercules (H, ‘ƙarfi’), Atlas (A, ‘juriya’), Zeus (Z, ‘ƙarfin iko’), Achilles (A, ‘ƙarfin hali’) da Mercury (M, ‘sauri’): S-H-A-Z-A-M, a nufinsa, wancan jarumin nasa ya tattarawa waɗancan siffofin. Ƙamus na Merriam-Webster (dictionary), sun bawa Kalmar ‘Shazam’ ma’anar, “canjawa ko bayyana (bayani) cikin gaggawa.” A wajen taron Pioneer’s Festival (2013), Chris Barton ya ce: “Kalmar Shazam na nufin, a duk lokacin kake wani abu, kamar siddabaru/tsafi”, ma’ana da suna kwatanta aikin ‘app’ din, da siffofin wancan jarumin (na comic).
Yadda Shazam yake aiki shi ne, idan ka sami wani sauti (na Qira’ar Alkur’ani ko waƙa), zaka buɗe manhajar Shazam, sai ka danna (clicking) a kan Shazam, zai na kaɗawa ‘mechanical wave’ yana ji (listening), yana naɗar wannan sautin, daga nan sai ya bayyana ma sakamako na sunan mawallafin sautin (artist, mis. Maher al-Muaiqly), sunan sauti (title, mis. الفرقان Al-Furqan), da sunan album ɗin sauti (mis. Alqur’ani), har ka iya kunnawa (amma fa sai ka buɗe ‘data’). Idan ya laluba sama da daƙiƙa 20 bai samu ba, sai yA ce ma “NO RESULT, TRY AGAIN” ma’ana, “babu sakamako, ka sake gwadawa.”
Shazam yana yin duk wannan aikin ne a ƙasa da daƙiƙa (millisecond) zuwa wasu ‘yan daƙiƙu (seconds) ta hanyar amfani da ‘Shazam Algorithm’, inda da zarar da an bashi damar neman wannan sautin da kake ji, ta hanyar ‘clicking’ akan ‘Shazam’ to nan da nan zai saki ‘Acoustic Signal’ (maneman sauti), daga nan kuma ya hau laluban sautin da ke masa kama da wannan sautin (spectrum). A inda kowanne sauti suna bashi ‘fingerprint/#’, kamar daina masu laluban mai laifi (a forensics) ko likitoci da 'DNA.'
Ga masu amfanin da wayoyin iPhone, za su iya sauƙe manhajar a ‘AppStore’ ta wannan link din:
https://apps.apple.com/us/app/shazam-music-discovery/id284993459
Ga masu amfani da wayoyin Android kume, ga link nan (kai tsaye) daga ‘PlayStore’:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.shazam.android
Bayan SHAZAM, akwai wasu apps da suke irin aikin da yake, kamar su SoundHound, Musixmatch, Soly, Music ID, ACRCloud, Axwave, Gracenote da sauransu.
© Aliyu M. Ahmad
29th Muharram, 1443AH
6th September, 2021CE
#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Hausa #Shazam
*Visual Credit: Audio Zone.
0 Comments