BABU MAI HANA A DAUKI RANKA IDAN MUTUWA TA ZO

 Idan baka da lafiya, ƴan uwanka za su iya kai ka asibiti, su tsaye ma, tare da taimakon Allah, don ka samu lafiya.

Idan ka shiga cikin rigima ko Shari’ah, za a iya tsaya ma har ka kuɓuta, ko a yi sulhu.

Idan matsalar kuɗi kake da, wani zai iya ara ma, ko ma ya baka kyauta.

Amma idan ka mutu, ba wani gata da duk wani masoyinka zai ma face a raka ka tare shi, su binne ka a rami, cikin kasa 😭.

Daidai da daƙiƙa ɗaya, babu mai ƙarama, don ka ƙara numfashi a duniyar nan.

Babu wanda za a yi sulhu da shi don a bar ka
Babu wani magani da zai hanaka mutuwa

Halinka da aikinka su kaɗai ne za su ja ma rahamar Ubangiji.

MUTUWA! Ita ce gaskiyar da mun sani, amma muke rayuwa kamar ba mu damu ba. In dai ka san zaka mutu, ka san akwai tambayoyin kabari, akwai azabar kabari, akwai tuhume-tuhume da ke kanka, da zarar waɗanda suka kai kabari sun baro maƙabarta.  

Allah Ya shirya mana aiyukanmu, Ya sa mu cika da imani.

(c) Aliyu M. Ahmad
27th Muharram, 1443AH
4th September, 2021CE

 


 

Post a Comment

0 Comments