Matuƙar kana iya ɓata awanni 2, 3 ko fiye a 'chats' da karanta 'statuses' da 'posting' a social media, ko kallo 'season films' na awanni 3 - 5 a kullum, to tabbas da zaka daure, zaka iya sadaukar da abin da bai fi mintuna 30 ba, wajen yin Adhkar na safiya/maraice, ko Tilawar littafin Allah Mai tsarki (Alƙur'ani), ko motsa jiki, ko karanta wani littafi da zai amfani duniyarka da lahirarka.
Yanzu mun shiga wani lokaci da ɗabi'ar nan da Bature ke cewa 'Reading Culture' (ɗabi'ar karance-karance) ta ja baya, a wajen mutane da yawa, tun bayan yawaitar wayoyin hannu, daga shekarar 2010 - 2015, zuwa yau, 2021 [Sabre, 2019].
Ko a manyan makarantu (universities/colleges); mu ɗalibai, mu kan kukan an bamu takardu (handouts) ko littafai masu shafi da yawa, mu ƙi karantawa, da sunan shafukan sun yi yawa. Abin lura, idan har zaka iya zama, ka ɓata 1 ɗaya a kana iya karanta 'comment(s)', masana suka ce; awa ɗaya ga mai ɗabi'ar karanta littafai, daidai take da karanta kalmomi 10,000 ko shafukan littafi 50 (50 pages) [Butler, 2014].
Shafuka 50 na iya karantuwa a wajen maras saurin karatu (slow reader) cikin awanni 3; ga matsakaici (average) awa ɗaya da rabi, ga mai sauri (faster) cikin ƙasa da awa ɗaya.
Lokaci! Shi ne kyauta mafi tsada da Ubangiji ya azurta bayi da shi. Kowa ya san, lokoci ba siyansa, ba kuma ya tariya (reverse). Manzon Allah ﷺ a hadisin "اغتنم خمساً قبل خمس", yana mana gargarɗi kan amfani da wannan dama ta rayuwa (lokaci). Don tun kana rayen ma, nauye-nauyen iyalin dake gabanka (reality na rayuwa), da wuya su barka ka yi atisayen gina kai, ta karatu, matuƙar baka gina ɗabi'ar ba tun kana matashi.
Idan kana zama da dattawa, in suna ma taɗin yadda suka yi asarar samaratarsu, tare da nuna takaici na rashin amfani da lokacinsu, wajen gina kai da kuma karatu, in ka kwatanta dalilinsu na baya da kuma halin da matasan yau ke ciki, za ka ga tazarar ba ƴar kaɗan ba ce. Sai dai gyaran Allah.
(c) Aliyu M. Ahmad
30th Muharram, 1443AH
8th September, 2021
0 Comments