Sau da yawa ba zaka san duniya (mutane) na ma kara ba, sai ka rasa iyaye. Iyaye sune hijabin darajarka duniya da lahira; hasali, sune sanadin zuwanka duniya. Waye ya nuna ma soyayya sama da ta su? Kullum burinsu ci gabanka, babu hassada balle ƙyashi.
Su ne za su ma kyauta ba don suna buƙatar (wani) abu a wajenka daga baya ba. Kai! Su kan iya rasawa, a wani lokacin don kai ka samu. Su ke ma addu'a a ɓoye dare da rana don kariya da ci gaban rayuwarka.
Kai! Yawancin alfarma ana maka ne saboda don mutuncin iyayenka. Misali, neman aure, aiki, zumunci; wallahi! Wani ko kulaka ba zai yi sai don darajar mahaifanka.
Ya aka yi kana ƊA, suna RAYE ka bar su cikin ƙunci? Wasu ma ko abin da za su ci yana gagarar su. Amma, ka san ka farantawa duniya (abokai, mata/budurwa), ka kuma manta da waɗanda suka kawo ka duniyar!
Kyautatawa iyaye DOLE NE! Daga bautawa Allah, da bin Annabi ﷺ, sai bi da kuma kyautatawa iyaye; babu wata biyayye da kyautatawa da ta fi wannan.
Duk yadda za a yi, ka yi ƙoƙari kyautata musu da yi ma su addu'a; don ba za ka iya biyan su abin da suka ma a rayuwa ba. Ka nuna musu soyayya da biyayya a asalin zahiri ba social media ba. DON, KOMAI YAWAN IBADARKA, DA TAIMAKAWA MUTANE, MATUKAR KANA DA MATSALA DA IYAYENKA, BA ZAKA SHIGA ALJANNAH, koda ko iyayen ba Musulmai ba ne.
© Aliyu M. Ahmad
10th Safar, 1443AH
18th September, 2021CE
2 Comments
Thank you for your admonition Malam Aliyu Ahmad may blessed you and entirely your families.
ReplyDeletefiddausisani37@gmail.com
ReplyDelete