Usman bin Affan رضي الله عنه ya ce: "Manzon Allah ﷺ ya kasance, idan an binne mamaci, ya kan tsaya akan ƙabarinsa ya masa addu'a, ya kuma ce (da sauran sahabbai):
استغفروا لأخيكم واسألوا له التثبيت فإنه الآن يسأل
Ma'ana: "Ku roƙawa ɗan uwanku gafara, ku roƙa masa tabbata, domin yanzu haka ana tambayarsa" [Sunan Abu Dawud, 3221].
Idan har ka damu da mutum bayan mutuwarsa, babu ƙaunar da zaka nuna masa sama da yi masa addu'a. Wannan ƙauna ce, tsakanin kai, da shi (mamaci), da kuma Allah. Idan ka shagala wajen nuna alaƙarka da shi, ko yaɗa hotunansa, wannan kuma tsakaninka ne da mutane, waɗanda kake neman attention ɗinsu, don shi mamaci, bai ma san kana yi ba.
Ba laifi ba ne, nemawa mamaci addu'a a 'social media', amma mu riƙa kiyaye wasu abubuwa kamar haka:
• Na farko:
Mu kiyaye ɗora hotunan mamaci, a yanayi na rashin daɗi ko jinya, ko hatsari; wanda inda yana da rai, ba zai so ganin hakan ba.
Mu kiyaye ɗora hotunan mata babu cikakkiyar sutura (hijabi, mis.), koda iyayenmu ne, ƴaƴanmu ko ƴan'uwanmu. Mu kiyaye ɗora hotunan matan aure, wanɗanda in da suna da rai, mazajensu ba za su so ganin wani ƙato yana yaɗa hotunan matarsa a social media ba.
• Na biyu
Mu kiyaye yaɗa sirrin chats da muka yi da shi/ita, wanda inda ya/tana da rai, ba zai/ta so ka yaɗa 'screenshot' na chats ɗinku ba, domin wannan cin amanar mamaci ne.
Abu Dawood (3207) da Ibn Maajah (1617) sun ruwaita cewa, Manzon Allah ﷺ Ya ce: "كسر عظم الميت ككسره حيا". Ma'ana "Karya ƙashin matacce, tamkar karya ƙashin rayayye ne."
Abul Walid Al-Baji رحمه الله yake cewa, ma'anar wannan hadisin shi ne, duk hukunci ɗaya ne, abun da zaka yiwa mutum a lokacin da yake raye, da lokacin da yake a mace" [Al-Muntaqa 2/63].
• Na biyu
Mu kiyaye aibanta mamaci, mu riƙa kame bakinmu daga faɗar laifukan da ya yi, a lokacin yana raye, domin in da yana da rai ba zai so ji ba. Mu shagaltu da nemawa mamaci gafarar Allah.
A cikin Bukhari (1367), Anas bin Malik رضي الله عنه ya bamu labarin cewa, wata rana suna zaune, sai aka zo wucewa da wata gawa, sai mutane suka yabe ta, suka faɗi alherin mamacin, sai Manzon Allah ﷺ ya ce "ta wajaba". Haka ma da aka zo wucewa da wata, sai aka faɗi aibin mamacin, sai Manzon Allah ﷺ ya ce "ta wajaba". Sayyadina Umar رضي الله عنه ya tambayi Manzon "mene ne ma'anar ta wajaba", sai ya ce: "waccan da kuka faɗi alherinta, Aljanna ta wajaba a gare shi, ita kuma wacce da kuka aibanta, kuka faɗi sharrin mamacin, wuta ta wajaba a kansa, (domin) ku ne shaidun Allah a bayan ƙasa."
• Na huɗu
Mu yi sani, faɗin 'Rest in Peace (RIF)' ba addu'a ba ce, malaman Musulunci da yawa su yi suka kan irin waɗannan kalmomi, gwamman ka yiwa mamaci addu'a kai tsaye, misali: رحمه الله, ma'ana, "Allah Ya masa rahama."
Abu na ƙarshe, in kuna ƙaunar ƴan uwanku da abokanku bayan sun mutu, za ku ci gaba da yi musu addu'a ne, har kuma lokacinku ya yi (ku mutu). Ba a iya kwanakin da ake juyayi ake taƙaita yiwa mamaci addu'a ba.
Allah Ya jiƙan waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, in ta mu ta zo, muma Allah Ya sa mu cika da imani.
(c) Aliyu M. Ahmad
9th Safar, 1443AH
17th September, 2021CE
0 Comments