Har yanzu, na kan raina hankalin mutanen da suke sharing na link, da cewa, in ka yi sharing zuwa group 5 ko 10, za a baka kyautar data, su kuwa su yi ta yi mana sharing, ta privates da groups.
Wasu links ɗin ma, in ka shiga, har bayanan mutum suke nema; phone nos, emails, NIN No, BVN..., su kuma ma su son bati su yi ta shigar da bayanansu 🤦♂
Magana ta gaskiya, babu wani website, hukuma ko gidan waya (MTN, AIRTEL, GLO..) da za su baka kyautar kuɗi, recharge cards ko data, wai kawai don ka yi sharing link ɗinsu. Kuskure mutane suke wajen bayar da bayanansu a yanar gizo, wai za a basu kyautar data, kana bawa scammers kyautar bayananka ne, za su kuma iya amfani da shi a duk lokacin da suka ga dama. Kar ka yi mamaki don an kwashe ma kuɗaɗe a banki, ko an hacking wani social media handle naka, duk ta wannan dalilin.
Allah Ya ba mu ikon kiyayewa,
Allah Ya tsare mu.
(c) Aliyu M. Ahmad
15th Safar, 1443AH
23rd September, 2021
#AliyuMAhmad #FasaharZamani
0 Comments