INFORMATION BROKER (IB)

Wai baka taɓa tunani ko mamakin lokacin da ka yi ‘chats’ da abokanka kan wani abu, kamar ‘computer’, ‘mota’, ‘sutura’, ‘wayar hannu (phone)’, ‘abinci’ ko ‘littafai’ a Whatsapp, Messenger, Telegram ko ta wata manhaja ba, bayan da ka zo Facebook, Instagram ko Twitter ka ga ana ma tallar wannan abun?

Information Broker (IB), ko Dillalan Bayanai a Hausa (wani lokacin ana ƙiransu data broker), kamfanonin fasahar sadawar ne na AdTech irin su Acxiom, Intelius, Experian, Epsilon, Datalogix, Exactis da suka kware wajen tattarawa tare da dillancin bayanan masu amfani da kafofin sadarwar (social media) ga wasu kamfanoni. Kamfanonin sadarwa na social media (irinsu su Whatsapp da Facebook) suna samun kuɗaɗensu yawanci ta hanyar siyarwa da waɗancan kamfanoni bayanmu, da muke chats ta sirri (private), ‘browse history’ daga ‘searching engine’ (kamar Goggle), ko abubuwan da muka fi bibiya a yanar gizo, game da abubuwan da muke so, kamar yadda na bada misali a sama, ko ta hanyar biyan kuɗin talla ‘sponsored’ kai tsaye.

MUTANE DA YAWA BA SU DA MASANIYA GAME DA WAƊANNAN KAMFANONIN, amma kuma da izininka (mai karatu) suke yi fa, saboda yana cikin dogon rubutun nan na TERM OF SERVICE da muke tsallake karantawa yayin sanya (installing) wata manhaja kamar Whatsapp, Facebook, Opera dss a cikin wayoyinmu, tare basu damar hulɗa da bayanan cikin wayarmu, kamar contacts da messages/chats.

Kamfanonin Facebook da sauran wasu social apps suna bibiyar bayananmu ta hanyar amfani da fasahar ‘artificial intelligence (AI)’ (الذكاء الاصطناعي) wanda ke amfani da tsarin ‘Algorithm’ wajen binciko bayani (data mining) daga ‘chats’ dinmu da bincike da muke a wasu kafofin (browse history). Ta yadda wannan fasahar kan iya tattara bayananmu cikin ƙanƙanin lokaci, misali; in ta sami ‘kalmomin ‘mota/car(Eng)/سيارة(Arb), sai ta turawa waɗancan kamfanoni (third party), kalmar mota (da muka ambata cikin chats ko browsing). Kalmar 'mota' ta yi daidai da abin da kamfanoni Leventis Motors, Innoson Motors da su Kaura Motors ke siyarwa (motoci), sai ka ga tallar motoci (sponsored) a ‘timeline’ na Facebook, ko ‘feeds’ na Twitter, ko ‘scroll’ na Instagram da TikTok da sauransu.

Duk maƙudan biliyoyin kuɗaɗen ka muke jin labarin Mark Zuckerberg (Facebook), Jack Dorsey (Twitter), Larry Page (Google), Zhang Yiming (TikTok) ke samu, suna samu ne ta hanyar siyar da bayananmu ga kamfanonin AdTech, da kuma karɓar talla ta kai tsaye (sponspored).

ABUBUWAN LURA

1. Ba kowanne bayanan sirri ne za mu riƙa ajiyewa, ko tattauna a kai ba cikin Social Apps ta chats. Shi ya manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa in za su tattauna wasu muhimman sirrika, ba sa yi online, wasu ma in an shiga ɗakin sirri ko ‘hall’, sai kowa ya kashe wayarsa. Wani meeting ɗin ma, haramun ne ka shiga da waya. Duk dai saboda tsaron ana iya siyar da bayananka ga wasu.

2. Mu kiyayi yawan ɗora kowanne irin ‘app’ cikin wayoyinmu, musamman na kyauta (free), ko waɗanda za su bamu damar kutsewa wasu (irinsu GBWhatsapp da VPN Apps), irin waɗannan sun fi siyarwa da AdTechs bayananmu.

4. Wayoyin kamfanonin Apple, Samsung da Google Pixel, sun fi sauran wayoyin bada kariya ga bayananmu (amma suma suna bada bawa 'data brokers' dama).

3. A matsayinka na mai hankali, ka yi nazari, idan har wasu kamfanoni da baka san da zamansu ba, suna iya kallo tare da satar bayananka, ina kuma ga Ubangijin da ya halicce ka, wanda yake cewa: "وهو معكم أينما كنتم" Mana’a, “(Ubangiji ) Yana tare da ku a duk inda kuke” [Al-Hadid, 4], kuma Manzon Allah yana cewa:  (اتق الله حيس ما كنت) كأنك تره فإن لم تكن تره فإنه يراك “ (Ka ji tsoron Allah a duk inda kake), kamar kana ganinsa, domin in kai baka ganinSa, to Shi yana ganinka.” [Bukhari, 50].

 

© Aliyu M. Ahmad

28th Muharram, 1443AH

5th September, 2021CE

 

#FasaharZamani #AliyuMAhmad #Hausa #Informationbroker

 

Post a Comment

1 Comments

  1. As'alullahal al'afwal aafiy fid duniya wal aakirah. Wannan zance haka yake dolane mutane mu rika kiyayewa waje wallafa dukkannin bayanan mu.

    ReplyDelete