MENE NE GIRMAN KAI?


Abin da wasu mutane suka ɗauka girman kai shi ne, rashin shiga cikin mutane, zaman majalissa, nisantar shiga sabgogin mutane da ba a gayyace ka ba (matuƙar ba don raini ba ne), ko sanya tufafi mai kyau/tsada (matuƙar ba don fariya ba ne); waɗannan duk a zahirin gaskiya ba girman kai ba ne. Da wataran zaka yi mu’amala da mutanen da ka ke yiwa zaton suna da girman kai saboda waɗancan dabi’u, da zaka tarar da saɓanin abin da kake zarginsu da shi. 

A HAƘIƘA GIRMAN KAI: cuta/jinya ce dake gurɓata zukata da tunani, wannan ya haɗa da:

1. Ƙin karɓar gaskiya ko juya mata baya, ko mutum yana jin ya fi ƙarfin yayi kuskure; ko

2. Jiji da kai da yawan taƙama da fariya da wata ni’ima ta Ilimi, yawan aikin ibada, dangi, kyau, mulki, dukiya da shuhura [Shifa’ al-Nufus p. 9] da yin gori da su; ko

3. Wulaƙanta mutane ko ɗaukar su ba a bakin komai saboda wani matsayi da mutum ya taka a rayuwa.

Ƙin karɓar gaskiya a lokacin da tabbata mutum ya yi kuskure babbar alama ce ta girman kai; ita gaskiya (daga Alƙur’ani ko Sunnah) ana karɓa daga wajen kowaye matuƙar gaskiyar ce. Irin wannan shi ne Annabi ﷺ Yake ce: " لا يدخل الجنة من كان في قلبه مثقال ذرة من كبر". Ma'ana "Mutum ba zai shiga Aljannah ba matuƙar akwai gwargwadon kwayar zarra na girman kai a cikin zuciyarsa" (Muslim 91). Masu juyawa gaskiya baya sune mutanen za su rayu cikin ƙunci (معيشة ضنكا) tun a nan duniya a tashe a ranar Alkiyama أعمي (Makafi) a gobe Alkiyama  [Daha aya ta 124].

Jiji da kai da nuna fifikon matsayi akan sauran mutane alama ce ta girman kai, kuma shi ne laifi na farko da Ibless ya yiwa Ubangiji bayan halittar Annabi Adam (AS), a lokacin da aka umarci Mala’iku su yiwa Adam (AS) sujjada, sai Ibless ya kada baki ya ce: “أنا خير منه خلقتني من نار وخلقته من طين” [Al-A’raf aya ta 12]; wannan ya ja masa ƙasƙanci da la’anar Ubangiji tun daga wancan lokaci har izuwa Tashin Alkiyama.

Wulaƙanta mutane, da raina su, ƙin amsa sallamarsu ko ƙira saboda ƙarancin shekaru ko talauci ko kawar musu kai duk don saboda kana da wani matsayi ko shekaru da suka haura nasu shi ma girman kai ne. Yana daga cikin nasihar da Lukman ya yiwa ɗansa: “ولا تصعر خدك للناس ولا تمش في الأرض مرحا إن الله لا يحب كل مختال فخور”; ma’ana: “Kada ka karkatar da kumatunka (fuska) ga mutane (in ka zo wucewa ko in sun ƙiraka), kada ka yi tafiya a ban ƙasa mai fariya, domin Lallai Allah ba Ya son mai taƙama da alfahari.” [Luqman aya ta 18].

Talakan kuwa da ba shi komai, amma ya ɗorawa kansa izza, taƙama da jiji da kai, yana daga cikin mutum 3 da Ubangiji ba zai ko waiwaice su ba a ranar Alƙiyama [Muslim 102]. Ɗorawa kai girman kai yaudarar kai ne, ɓata ne, kuma yana jawowa mutum ƙasƙanci da halaka a duniya da lahira. Babban laifi ne ka ɗorawa mutum girman kai don baya mu’alama da kai, matuƙar ba girman kan ne da shi ba, Gheeba ne Kazafi ne.

Girman kai bashi da magani face komawa ga Allah, Yin imani da gaskiyar da ta zo cikin littafinsa da sahihiyar Sunnah, da ɗaukar kai ba komai ba. Allah Ya mana tsari da girman kai, da duk dangin cututtukan zuci 🤲

(c) Aliyu M. Ahmad
21st Safar, 1442AH 
9th October, 2020CE

Post a Comment

0 Comments