TikTok

 



Kamar sauran manhajoji na social media, TikTok na ɗaya daga social apps da wani ɗan China, Zhang Yiming ya ƙirƙira a 2016. Tiktok na bawa maabota amfani da shi damar sakin bidiyo na irin baiwar da Allah Ya ba su na kimiyya, kirkire-kirkire, hikima, abubuwan mamaki, dafe-dafe, nuna halittun namun daji da na ruwa, tsaunuka, tallace-tallece da sauransu, cikin ‘yan sakanni/mintuna. A yanzu haka, akwai masu amfani da manhajar Tiktok sama da miliyan 700 a fadin duniya (Data Reportal, 2021).

Kamar yadda kowacce manhaja za a yi amfani da ita ta hanyar da ta dace ko akasin haka. Misali, a social media za mu iya sada/haɗa zumunci da ‘yan uwa, abokai da wanɗanda ra’ayinmu ya zo ɗaya, a karatu ko kasuwanci/aiki, wallafa wa’azi ko nasiha, ko sanya karatun Alqur’ani ko wani ilimi na addini ko rayuwa, nishaɗi wanda bai saɓawa addini da al’ada ba, bayyanawa duniya irin baiwar da Allah ya mana, ko tallata kasuwancinmu da sauransu. Wanda yake da followers, samun comments da likes masu yawa, zai iya sami kudin sosai a TikTok (Dilon, 2020).

Kwanan nan ake maganar Khaby Lame (Charli D'Amelio), dan ƙasar Sanegal, mazaunin Italy, da yake wallafa bidiyon ban dariya (fun), aikace-aikacen gida dss a TikTok, wanda yanzu haka yana da followers sama da miliyan 100, kuma maganar da ake, profile dinsa ya kai ƙimar $2m (N822,719,920.00) (TheWikiFed, 2021).

Sai dai abin takaici, duk da waɗancan abubuwa da za mu iya na alheri, na ƙaruwa, samun lada, karatu, ƙara wayewa, da samun kuɗi; sai ga shi yawancin masu amfani da manhajar Tiktok suna yin abin da yasa, a da muke yiwa ‘yan film, kallon mutane banza; saboda raye-raye. Wasu har fiye da yadda muke tsammatawa ‘yan film suke na raye-rayen banza, cikin sutura ta rashin kamala da kunya, waɗanda da suka saɓawa dabi’un addininmu da al’adarmu (akhlakul karimah), wasu ma tsir*-tsir*, wa’iyazu billah. Kuma ‘ya’yanmu ne, ‘ya’yan Hausawa, Musulmi, musamman ma mata. Yarinya na tsageranci ana zuga ta, tana ƙara feƙewa. Saboda wallafa irin wadannan abubuwan fitsarar fa, ko a baya-bayan nan ƙasashen Indonesia, Bangaladesh, India, Pakistan, Misra (Egypt) sai da suka dakatar da amfani da TikTok na ‘yan kwanaki (TechCrush, 2020).

Cikin hadisin Bukhaari (3484), daga Abu Mas‘ood; Annabi ya ce:

إذَا لَم تَستَحيِ فَاصنَع ما شئت

“Idan baka jin kunya to ka aikata abinda ka ga dama.” Annabi ya fadi cewa:

كل أمتى نعافى إلا المجاهرين

“Dukkan zunuban al’ummata za’a yafe musu laifinsu (idan sun tuba) face na masu bayyana laifi (mujahara) (Bukhari,5721 & Muslim 2990).

Hakanan, masu bi suna kallen-kallen wannan fitsarar, Annabi ya faɗi cewa "فزنا العين النظر” (Bukhari, 5889). Kuma Allah cikin Alkur’ani ya gargaɗin mummunai, da su rinƙa rintse idanunsu daga kale-kallen na haram da duk abin da zai kai su ga fitina (Nur, aya ta 30 & Isra’ aya ta 32).

TikTok da sauran manhajojin sada zumunta na zamani (Social Media Platforms) an yi su ne da kyakkaywar manufa, waɗanda suka yi, sun yi manhajojin ne don yin talla da samun kudi, amma wasu ke amfani da su wajen bayyana rashin ɗa’a da tsageranci. Wannan kuma haƙƙi ne akan iyaye tseratar da iyali daga saɓo (Tahrim, 6), kuma haƙƙi ne akan hukuma tsarewa al'umma tarbiyarta.

 

Allah Ya shirya mana zuri'a.

 

© Aliyu M. Ahmad

12th Muharram, 1443AH

21st August, 2021CE




Post a Comment

0 Comments