RAYUWA MAI CIKE DA DARASI


Kowacce rana in ta ɓullo, kowanne mutum da ka yi mu'amala da shi, kowannen labari da kunnenka ya ji, kowanne al'amari da ya faru a gaban idonka, akwai darussan da suke son/ƙoƙarin koyar ma, na gyara ko ƙara himma, sai dai in baka shirya ɗauka. Darasin rayuwa, ba sai iya cikin littafi ba. 

Jiya ina kwance a gida, jiki babu kwari, na fito da nufin da zan ɗau ruwa a fridge, sai Umma ta ke ce min, yau gidan ba kowa, Mahmud da Ahmad (Malam) ba sa nan, ba mai zuwa min kasuwa, ga shi kai kuma baka jin daɗi sosai (Allah Sarki Uwa).  Na ce "Umma kawo sautun, zan je miki kasuwa yau. Rabona da zuwa kasuwa, dama na dauki 'yan shekaru kam, yo! Ko don na ɗan ware kafa ta ma, da kafata zan je." Na karɓi sauto, na tafi kasuwa.  

A hanyar dawowa ta na gamu da abin da ya jima yana ban mamaki, abin da na jima ban rubuta irinsa a 'DIARY'na ba, kuma ya ban darasi da mamakin da sai da na ɗauki lokaci ina jinjina abin nan. SABODA DA DARASIN CIKINSA, NA GA YA CANCANCI NA EXTRACTING DAGA DIARY. 

Faruwar lamarin, na zo wucewa ne ta wata kwana cikin kasuwa, wajen layin masu markade, sai wani dattijo ya zo wuce, sai na raɓe na bashi hanya ya wuce. Ta bayansa, a ɗan gefen hanya kuma, wasu yara ne guda biyu, a ido zan iya kwatanta su da 'ƴan shekaru, tsakanin 11 zuwa 13. Ɗayan zai wuce, sai ɗayan ya jawo hannunsa, ya rike shi, ya ce masa "KAI TSAYA MAN YA WUCE (wato), SHI MA BAKA GA SAI DA YA TSAYA WANCAN TSOHO (DATTIJO) YA WUCE BA."

Na jima ina mamaki wannan lamari, 'aiki da sakamako' cikin ƙasa da daƙiƙa ɗaya 🤔. Na farko na ga tausayin a idon uwa. Hakuri da aikata alheri, komai kankantarsa, bature na cewa; “what goes around, comes around”, don na ga tukwuicin alheri a nan take. Na ga kuma tasirin aboki na gari (a tskanin yaran nan).

Sai na tuno faɗin Ubangiji:  “هل جزاء الإحسان إلا الإحسان” (Arrahman, 60), Ubangiji ﷻ ya kara da cewa cikin Aali-Imran (148), game da mutanen da suke neman dace: “Allah zai saka musu da sakamakon duniya da kuma kyakkyawa a lahira, domin shi Allah, yana son masu kyautatawa”, da kuma wani hadisi/sanannen ƙauli “كما تدين تدان”, da wani karin magana da Diane Keaton (Kay Adams) cikin film ɗin 'The Godfather' (1972)  "RESPECT IS EARNED, NOT GIVEN". 

Alhmadulillah! Mu dama al’adarmu ta Hausa, girmama manya dabi’armu ce (Alhassan, et al (1982) cikin Zaman Hausawa), kuma addininmu ya mana umarni da girmama waɗanda suka ɗaremu a shekaru, musamman masu furfura (tsofi). Haƙiƙa in kabawa wanda Allah ya bawa girma, ka garjanta su (musamman iyaye da dattawa), da sannu kaima Allah zai ma sakanya ma tun a duniya.


© Aliyu M. Ahmad

15th Muharram, 1443AH

23rd August, 2021CE

Post a Comment

0 Comments