ME YAFI WANNAN CIWO? 🥺
A ce kana mahaddacin Alƙur'ani, ka yi ƙoƙarin jan wata aya, ka yi, ka yi, taƙi zuwa 😭 saboda sakaci, wayyo 🤦♂️
Amma kasan gwamma wancan ma!
May be shi in ya buɗa fallen Alƙur'ani yana iya tada baƙi ya karanta.
Ina ga mutumin da ya kai munzali na mutum (shekaru), kuma zuciyarsa ba komai na Alƙur'ani. Ace kana iya karanta wannan saƙon, amma baka iya karanta ko kalma ɗaya cikin Alƙur'ani Maigirma! 🤔 Kana Musulmi!
Cikin Suratul Furqan, aya ta 30, Manzon Allah ﷺ Ya kai ƙarar mutane wajen Allah, tun wancan lokacin, shekaru sama da 1000 kan ana ƙauracewa Alƙur'ani:
وقال الرسول يا ربي ان قومي اتخذوا هذا القرآن مهجورا
Ibn Qayyim رحمه الله yake cewa, yana daga cikin ƙauracewa Alƙur'ani, ƙin koyonsa, ƙin karanta shi/tilawarsa, ƙin tadabburi da shi, ƙin aiki ko hukunci da shi dss (Alfawa'id, p. 82).
Mu sani!
• Karatun Alƙur'ani shi ne mafi ƙololuwar zakiri (Fiqh al-adiyya waladhkaar (1/50).
• Bambancin gidan ake ambaton Allah, da gidan da ba'a ambaton Allah, kamar rayayye ne da matacce (Muslim, 779).
• Duk harafi ɗaya ka karanta kana da lada goma da ninki (Tirmidhi, 2910).
• Karanta Alƙur'ani, yana yaye ƙuncin dake cikin zukata (Yunus, aya ta 57)
• Waɗanda suke tilawarsa, haƙiƙanin karatunsa, sune suna masu imani da shi (Baqara, aya ta 121)
• Ma'abotanshi (masu karanta shi), za su sami ceto a ranar Alƙiyama (Muslim, 804).
• Annabi ﷺ Ya mana bushara, da mafi alheri cikin mutane, shi ne wanda karanci Alƙur'ani, kuma yake karantar da shi (Tirmidhi, 3154)
Abun alfahari ne a wajen Musulmi ya iya karanta Alqur'ani, falala ne haddace shi. Abin kunya ne, Allah Ya azurta ka da iya karanta baƙin Alƙur'ani, ka ƙauracewa TILAWARSA ko SAURARONSA har na tsawon kwanaki, watanni ko ma fiye da shekara.
Ka kan iya buɗe Facebook ko wani chat na awanni, amma baka iya buɗe Alƙur'ani na mintuna 10. Ka kan iya sauraren waƙe-waƙe, ko kallon season, amma baka iya kunnawa da sauraron Alƙur'ani na minti 10, abin taƙaici! 😥
Abin kunya ne rashin iya karanta da shi, rashin koyonsa, da rashin tilawarsa akai-akai. Abu ne mai kyau kana Musulmi, kana ƙoƙarin koyon Alƙur'ani a wajen malami, koda da aya ɗaiɗai ne a kullum.
YA YA ALKARKA/KI DA ALQUR'ANI?
Ina roƙon Allah Ya azurta mu da Alƙur'ani, tilawarsa, tadabburinsa, da cetonsa a ranar Alƙiyama, amin.
(c) Aliyu M. Ahmad
10th Muharram, 1442AH
19th August, 2021CE
0 Comments