MATSALOLIN DA SUKA SA, BA ZA MU GA CI GABA BA


1.  Da yawa cikin mutane in suka samu dama, kowa tunaninsa iya kansa ne, ba al'ummarsa ko yankinsa ba. Wani fa in ya samu dama, bai ƙi kowa ya mutu ba, don shi ya rayu, ba kuma zai iya sadaukar da kansa ba, don al'umma su rayu. Ɗaiɗaiku ke ƙoƙarin kamantawa, cikin waɗanda Allah Ya bawa dama, da cikin manyan ma'aikatan gwamnati da ƴan siyasa.

2. Kowa yana raina baiwar da Allah ya ba shi, cewa, sai masu kuɗi ko mulki ne za su iya warware matsalolin da suke tattare a yankinmu. Da zamu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe, za mu iya magance wasu daga cikin ƙananan matsalolin da ke dabaibaye da mu a yankinmu, kamar tsaftar muhalli, ilimi da tarbiyya, ruwan sha, taimakekkeniya da sauransu.

3. Marasa ƙarfi basa tunanin laluban hanyoyin da za su karya alƙadarin talauci. Wani tunaninsa an haife a talauci, a talauci zai mutu. Haka nan, wasu daga cikin matasa sun kashe zukatansu, suna jiran zai sun sami gurbin aiki a cikin gwamnati. Allah Ya yalwata ƙasa da arziƙi, ya cika kwakwalen mutane da fikira, nauyi ne da ya rataya a yuwanmu, amfani da duk wata baiwa da dama da Allah Ya bamu a ban ƙasa wajen laluban arziki, sai Allah Ya taimake mu, Ya kuma azurta mu. 

4. Rashin bawa waɗanda suka cancanta dama a aiyukan ci gaban jama'a (gwamnati), sai ɗanwane-da-wane. Marigayi Mallam Aminu Kano (1920 - 1983) ya ce: "A zaman duniya Allah ﷻ ya halicci kowanne ɗan-Adam da baiwar sa kuma da hikimar daya sani. Zamu bawa kowa gurbin da zai bada gudunmawa, badan shi ɗan wane ne ba ko, badan an tsangwame shi ba, ba sai ya bada hanci ba ko ya zagaya da mu ba. Kowanne mutum yanada darajar sa". A wani ƙaulin nasa ya ce: "Nijeriya ba zata taɓa zama lafiya ba, har sai wanda ba ɗan kowa ba, ya zama kowa, ba tare da ya san kowa ba."

5. Hassada, kyashi da ƙiyayya sun dabaibaye zukatan mutane. Mutane sun ɗauƙi ɗabi'a ta burbushin Jahiliyya na nuna bambancin yanki. Mun bar zumunci, sai ga wanda zai amfane mu. Ba ma taimakawa juna, sai in muna tsammanin ramko daga wanda za mu taimakawa, bada tallafi ko kyautatawa.

6. Uwa-uba, mun bar Allah mu kama son zukatanmu. Duk wani hani na Shari'a mun bi mun take; tauye mudu, yaudara da ha'inci da zamba cikin mu'amala, tauye haƙƙin iyali, karɓar cin hanci da rashawa, ga yaɗa alfasha da fasadi a bayan ƙasa, to ta ya zamu ga daidai?

Ubangiji ﷻ Yana faɗi cikin Alƙur'ani: "Ɓarna ta bayyana a cikin ƙasa da teku, saboda abin da hannãyen mutane suka aikata. Domin Allah Ya ɗanɗana musu sashin abin da suka aikata...." 

[سورة الروم: 41]

Ibn Qayyim Al-Jawzy رحمه الله ya ke cewa: "Sababbin duk wata damuwa abubuwa ne guda biyu: (1) Son duniya, da maida hankali na son sai an sameta ta kowacce hanya, (2) Sakaci da aiyukan alheri da ɗa'a (kamar taimakekkeniya a tsakanin mutane, dss)" 

[عدة الصابرين ص 265]

Matsalolinmu, ba za su irgu ba. Kullum, komai ƙara taɓarɓarewa yake, kuma ba a daina ɓarna a bayan ƙasa ba, ko yaushe za mu farka? In za mu shekara dubu muna lissafa matsalolinmu, da hanyoyin warware su, matuƙar ba a ɗauki mataki a aikace ba, sai dai kullum su ci gaɓa da faru, sabbi kuma suna ɓullowa.

Allah Ya gyara mana halayyarmu, Ya bamu zaman lafiya da yalwar arziƙi, amin. 

(c) Aliyu M. Ahmad

16th Muharram, 1443AH

24th August, 2021CE




Post a Comment

0 Comments