Idan ka nutsu, ka duba, yawancin waɗanda suke mutuwa A YAU, sai ka ga babu wata jinya a tattare da su. Wasu hatsarin abin hawa ne ya rutsa da su, wasu fuju'a, wasu ruwa ya tafi da su, wasu sun faɗa hannun ƴan ta'adda, ƙaddara ce babu mai dabarar ƙauce mata.
An ruwaita daga Anas bin Malik, Annabi ﷺ Ya ambata cikin alamomin dosowar tashin alƙiyama, akwai yawan mutuwar fuju' (yau/yanzu kuna tare da mutum, jimawa kaɗan a ce ma ya mutu, ba tare da wata jinya ba) ba a yi a yau?
Ban sani ba ko NI da KAI mun shirya?
Kar ka taɓa tunanin sai ka kwanta jinya ne mutuwa za to ma. Sanadinta na da yawa. Baƙuwa ce wacce bata sallama. Da zaran lokacinka ya yi zata ziyarce ka, ta cika umarnin Tabarakahu Khaliƙi.
Darasin mutuwa a bayyane yake, babu wanda bai san gaskiyarta ba, da jahili da mai ilimi, da mai mulki da mabiya, da talaka da mai arziƙi, har da dabbobi, tsutsuye da tsirrai. Har Bature na mata karin magana da "Death is the painful truth."
Hanya ɗaya da zata zo ma da sauƙi, ita ce, ka fara shirin taryar baƙuwarka tun yau, tun yanzu da aiyukan alheri, da nesantar na aiyukan sharri da cin haƙƙin mutane (na dukiya ko cikin zance).
لو كانت الدنيا تدوم لاهلها لكان رسول الله ﷺ حيا وباقيا، ولكنها تفني ويفني نعيمها وتبقي المعاصي والذنوب كما هي.
Allah Ya sa mu cika da imani.
نسألك يا الله ان تشفي مرضان وترحم موتان وأن تغفر ذنوبنا أجمعين.
0 Comments