MU FADAWA KANMU GASKIYA




Ba abu mai wuya irin faɗawa kai haƙiƙanin gaskiya, ka karɓa, ka kuma yi aiki da ita, komai ɗacinta.
Rayuwar nan kowa ya san daga haihuwa ce zuwa mutawa, amma in zaka mutun ma a bar ka ka mutu da mutuncinka man da daraja. Rayuwa cikin ƙasar nan na cike da ƙalubale da jarrabawa, a bar ka da ƙaluɓalen neman na abin da zaka ci ma man, ba fargaba da tsoro.

Cikin lissafin matsalolin da ƴan ƙasa ke ciki, in ka ɗauke rashin ingantattun kayan more rayuwa, ilimi, kula da lafiya, hanyoyin sufuri, tarbiyyar al'umma da adalci. A shekarun baya matsalar ƴan bindiga daga Gabas zuwa Zamfara mu ke jin ta, a hankali ta matso Katsina, Sokoto da Kaduna... abin har da garkuwa (kidnapping) Allah dai ya tsare, idan ba mu farkar da jagarorinmu (waɗanda haƙƙin kare rayukanmu, dukiyoyinmu da mutuncinmu suka rataya a yuwansu) yanzu ba babu wanda ya tsira kaf cikinmu (Allah Ya kiyaye).

Yau har ta kai kana cikin gidanka za a ma waya, a baka wa'adi na za a zo a tafi da kai. A kashe iyalinka, a musu fya*e, a kwace duk abin da ka tara. Kuma babu garkuwa ko ɗaukar hukunci daga mahukunta. Kullum cikin fargaba muke.

Mu ajiye bambanci, ɓangaranci, ɗora laifi, mu fuskanci wannan matsalar, wannan matsalarmu ce baki ɗaya. Muna zaman lafiya ana neman rayukanmu, dukiyoyinmu da mutuncin iyalanmu. Haƙiƙa akwai wata ƙulli na son a ɗaiɗaita mu, a samu cikin mawuyacin hali, galabaitattu. Yau in an yi can da can, da sannu (Allah Ya kiyaye) a nan za a yi. In an yiwa wancan yau, gobe (Allah Ya kiyaye) ni da kai bamu tsira ba.

To amma abin haushi, duk sanda wata matsala ta taso, maimakon mu fuskanceta, muna da yawa, da murya, mu ja hankalin mahukunta, sai mu juya akalar caccaka kan ƴan uwanmu. Kowa na ɗorawa kowa laifi. Su kuwa waɗancan azzaluman in sun zo, ba ruwansu da kai ɗan APC ne ko PDP, nai kuɗi ƙo talaka, Musulmi ko Kirista, jahili ko mai ilimi, burinsu su tagaiyara kowa ne kawai. Maimakon mu tsaya mu yaƙi matsalolin dake kewaye damu, sai kuma mu buɗe sabon shafin cin mutuncin juna da ɓata fikirarmu kan #Taliban #Afghanistan (wata matsalar kuma daga can Gabas Ta Tsakiya).

Mu ta tattagen neman hago wasu matsaloli daga wata duniyar, bayan ga namu matsalolinmu nan jingim, mun kasa warwarewa, zamu ƙarar da fikarar tunaninmu wajen karewa ko tofa albarkacin baki a matsalar dake can nesa da mu. Mu faɗawa kanmu gaskiya, tun duniya na mana ƴar manuniya. Haƙika muna cikin matsala, rashin tsaro, fargaba da fatara... ya za a yi mu warware waɗannan?
Allah Ya bamu zaman lafiya.

- Aliyu M. Ahmad
16th August, 2021

Post a Comment

1 Comments

  1. https://www.smfclyrics.com/2022/04/khaby-lame-bio.html

    ReplyDelete