MA’ANAR IFTAR
Kalmar ‘Iftar’ (إفطار)kalmace ta larabci da aka juyota
daga kalmar "الفطور" ma’ana
(Kari/breakfast). Ita kuma kalmar ‘IFTAR’ shi ne cin abincin da masu Azumi suke
ko sha bayan faduwar rana a watan Ramadhan ko waninsa (Ibn Manzur, Lisal
al-Arab shafi na 3435 (Juzu’i na 5/232), Hans Wehr shafi na 739).
LOKACIN YIN BUDA BAKI (IFTAR)
Fadin Allah (S.A.W.); Alkur’ani Suratul Baqara aya ta 187:
…ثُمَّ
أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِ…
Fassara:
“…Sa’an nan
kuma ku cika azumi zuwa ga dare...” - Baqarah
aya ta 187
An karbo hadisi daga Anas bin Malik:
"إن النبي صلى الله عليه وسلم، لم يكن المغرب حتى يفطر ولو على شربة ماء"
Fassara:
“Manzon Allah (S.A.W.) Ya kasance baya Magriba; har sai ya yi buda-baki
(Iftar) ko da ko da shan ruwane” – Tirmidhi
DARE/FADUWAR RANA
Dare ko kuma faduwar rana, shi ne lokacin da rana ta juya izuwa
yamma (غرب),
yayin da gari ya fara duhu ta gabas, ta yamma kuma gari yana yin fatsi-fatsin ja,
daga nan kuma kadan-kadan sai duhun ya game gari gaba daya (غروب)
– Duba Guzurin Ramadan rubutu na 10 (Part X).
ABUBUWAN DA AKE YIN IFTAR (BUDA BAKI) DASU
An karbo hadisi daga Thabit Al-Bunani, cew ya ji daga Anas ibn Malik Ya
ce:
"كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يفطر على رطبات قبل أن يصلي، فإن لم تكن حسا
حسوات من ماء"
Fassara:
“Manzon Allah (S.A.W.) Ya kasance yana buda baki da kayan marmari
(fruit) kafin yayi Sallah, idan babu kayan marmari sai ya yi da dabino, idan
babu (dabidon) sai ya kamfaci ruwa” – Abu Dawud, hadisi na 2356
An karbo hadisi daga Salman bin Amir; Manzon Allah (S.A.W.) Yace:
"إذا كان أحدكم صائمًا فليفطر على التمر، فإن لم يجد التمر ععلى الماء فإن الماء
طهور"
Fassara:
“Idan dayanku ya kasance Mai azumi, sai yayi buda baki (iftar) da
dabino, idan bai sami dabino ba sai yayi da ruwa, domin ruwa ya kasance mai
tsarkine”- Abu Dawud,
hadisi na 2355
A ruyar Anas ibn Malik cikin Jami’at Tirmdhi hadisi na 694,
Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:
"من وجد تمرًا فليفطر عليه، ومن لا؛ فليفطر على ماء فإن الماء طهورٌ"
FALALAR YIN IFTAR (BUDA BAKI)
An karbo hadisi daga Sahl bin Sa’id; Manzon Allah (S.A.W.) Yace:
"لا يزال الناس بخير ما عجلوا الفطر"
Fassara:
“Mutane ba za su gushe cikin alkhairi ba, matukar suna gaggauta yin buda
baki” – Tirmidhi, hadisi na 699
ABIN DA AKE
FADI (ADDU’A) A LOKACIN YIN BUDA BAKI
An karbo hadisi
daga Marwan ibn Salim Al-Muqaffa (R.A.); … Abdullahi ibn Umar (R.A.) Ya ce: “Manzon
Allah (S.A.W.) Ya kasance idan ya zo yi buda baki Ya na cewa:
"ذهب الظمأ وابتلت العروق وثبت الأجر إن
شاء الله"
Hausar Arabiyya
(Transliteration):
“Dhahabaz-zama’u
wabtallatil ‘uruqu wa thabatal-ajru in sha Allah”
Fassarar Hausa
(Translation):
“Kishirwa ta
tafi, jijiyoyi sun jiku, kuma lada ya tabbata in Allah Ya so”- Abu Dawud, hadisi 2357
__________
To be continued
…. in sha Allah
1st Ramadan, 1438 AH
(27th May, 2017
AD)
0 Comments