Lokacin kamewa na
Azumi shi ne tun daga fitowar Alfijir na gaskiya, har izuwa faduwar rana, kamar
yadda ya zo karara cikin Al-Qur’ani Mai Girma, inda Allah (S.W.T.) Ya fada
cikin Suratul Baqarah aya ta 187:
...وَكُلُواْ
وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ
ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِ…
Fassara:
“…Kuma, Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku
daga silili baki daga alfijiri. Sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare...” - Baqarah aya ta 187
Abin nufi shine: a cikin kwanakin Ramadhan (kwanakin yin Azumi
kenan); masu Azumi za su ci, su sha da daddare har zuwa lokacin da Alfarijir
zai fito, sannan da zarar Alfijir ya bayyana kuma lokacin Azumi ya shiga har
izuwa faduwar rana (wato Magriba).
MA’ANAR FARIN ZARE DA SILILI (BAKIN ZARE DA FARIN ZARE)
An karbo hadisi daga Adiyy bin Hatim (R.A.) cikin Bukhari Hadisi na 1916 ya ce:
قال
لمانزلت: " حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ
ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ" (Baqara: 187) ؟ عمدت غقال أسود وإلى عقال أبيض، فجعلتها تحت وسادتى، فجعلت أنظر فى
الليل، فلا يستبن لي، فغدوت على رسول اللع (صلى الله عليه وسلم) ذكرت له فقال:
"إنما ذلك سواد الليل وبياض النهار".
Fassara:
Adiyyu ibn Hatim (R.A.): Yace “A lokacin aya ta sauka cewa: “حَتَّىٰ
يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ
ٱلۡفَجۡرِۖ”. Sai na dauki bakin
zare da kullin farin farin zare na sanya su karkashin matashi na. Na rika dubawa
acikin dare babu abinda ya bayyana mini, sai na tafi zuwa ga Manzon Allah
(S.A.W) na ba shi labarin haka, sai Ya ce: “Abin da ake nufi da duhun dare da
hasken yini” - Bukhari Hadisi na 1916
ALFIJIR
Ibn Munzir, Lisal al-Arab shafi na 3351:
“Alfijir shi ne ja-ja rana (da yake fitowa)
a karshe duhun dare”.
A takaice, Alfijir wani dan jan ko kyalli hasken rana ne wanda yake
dallowa daga mahudar rana a karshen dare, wanda daga shi sai gari yayi duku-duku
(twilight/شفق), sai fitowar fitowar
rana (sunrise/شروق), sai safiya (morning/صباح), sai hantsi (lokacin sallar duha) sai kuma rana takewar rana (زوال). Alfijir a Turance ana kiransa da “dawn”.
KASHE-KASHEN ALFIJIR
Alfijir ya kasu kaso biyu: (1). Alfijir na
karya; da (2) Alfijir na gaskiya
1. ALFIJIR NA KARYA:
Alfijir na karye shi ne kyalli, ko dan
dushu-dushu daga mahudar dake bayyana a karshen duhun dare, wanda daga baya inda
zaka kara daga kai da kallo zuwa mahudar rana zaka iya rasa shi tamkar ba’a yi
shi ba, wannan yasa ake ce masa Alfijir Na karya.
Hukunci;
Ba ya hana a cigaba da yin sahur (cin abinci, ko shan abin sha, ko saduwa da
iyali), sannan ba ya halasta a sallaci Sallar Asubahi, ko a fara Ibadar Azumi.
2. ALFIJIR NA GASKIYA
Shi ne ja-ja da mai dan dum (dark red) daga
inda mahudar rana take wanda daga ya fito zai rika budewa gari yana kara haske,
har ka iya ganin nesa, har rana ta fito.
Hukunci:
Da zarar ya fito shi ne yake haramtawa masu
Azumi ci da sha (ma’ana farawar lokacin ibadar kamewa [azumi] na ranar), har izuwa faduwa rana, sannan kuma yake wajabta
sallatar Sallar Asubahi.
DARE/FADUWAR RANA
Dare ko kuma faduwar rana, shi ne lokacin da rana ta juya izuwa
yamma (غرب),
yayin da gari ya fara duhu ta gabas, ta yamma kuma gari yana yin fatsi-fatsin ja,
daga nan kuma kadan-kadan sai duhun ya game gari gaba daya (غروب).
Faduwar a Turance shi ake cewa 'sunset'
Hukuncin Faduwar Rana/Shigar Dare:
Wanna
lokacin shi ne yake nuna halaccin mai Azumi yayi buda baki a Ramadhan ko Azumin
nafila, da kuma lokacin wajibcin sallarta Sallar Magariba ya shiga.
A taikace wannan shi ne dan takaitaccen bayani game da lokaci KAMEWA ga
mai Azumi, tun daga fitowar Alfijir na gaskiya (Alfajr As-Sadiq) har izuwa dare/faduwar rana
kamar Allah (S.W.T.) Ya fadi:
...وَكُلُواْ
وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ
ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِ
Allah ne mafi sani.
__________
To be continued
…. in sha Allah
21st Sha’aban,
1438 AH
(18th May, 2017
AD)
0 Comments