GUZURIN RAMADAN XIII: SAHUR



MA’ANAR SAHUR
Sahur shi ne cin abinci da shan abin sha; ko madara a lokacin sahur (kafin bayyana Alfijir da niyyar Azumuntar ranar) kamar yadda الأزهرى ya fadi cikin littafin ابن منظور wato لسن العرب shafi na shafi na 1985 (Juzu’i na 3 shafi na 482).


LOKACIN YIN SAHUR
Ana yin sahur ne a karshen dare, kafin fitowar Alfijir kamar yadda Allah (S.W.T.) Ya fadi a cikin Alkur’ani, Suratul Baqara aya ta

...وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ

Fassara:
“…Kuma, Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijiri...” - Baqarah aya ta 187

An karbo hadisi daga Zaid in Sabit (R.A.) Yace:

"تسحرنا مع رسول الله صلى الله عليهم وسلم، ثم قمنا إلى الصلاة. قلت: كم كان قدر ما بينهما؟ قال خمسين آية"

Fassara:
“Mun taba yin Sahur tare da Manzon Allah (SAW) sa’an nan muka mike zuwa ga sallah, sai na ce: “Gwargwadon nawane lokacin da ke tsakaninsu (Sahur da sallah)? Ya ce: “Gwargwadon karatun ayoyin hamsin” – Sahih Muslim, hadisi na 2552

An karbo hadisi daga Samura ibn Jundab; Ya ce: “Na ji Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"لا يغرن أحدكم نداء بلال من السحور، ولا هذا البياض حتى يستطير"

Fassara:
Kada kiran sallar Bilal ya hana dayanku Sahur dinsa, kuma ko da wannan farin hasken (Alfijir na Karya) har ya mike (ya bayyana)” – Sahih Muslim, hadisi na 2596; a wata ruwayar kuma (hadisi na 2547): "حتي ينفجر الفجر" (ma’ana har sai Alfijir ya bayyana)

A cikin wata ruwayar ta Imam Ahmad:

"لا تزال أمتي بخير ما عجلوا الفطر وأخروا السحور"
Fassara:
“Mutanena ba zasu gushe suna kan alkhairi ba; matukar suna gaggauta buda baki (Iftar), kuma suna jinkirta Sahur” – Imam Ahmad 5/174

An karbo hadisi daga Abu Hurairah (R.A.); Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"إذا سمع أحكم النداء ولإناء على يه فلا يضعه حتى يقضى حاجته منه"
 سنن الدار القطني (باب فى وقت السحر): 2207


ABUBUWAN DA AKE YIN SAHUR DASU
Ana iya yin Sahur da dukkan dangogin abinci, da kuma abin sha; kuma ya kamata jama’a su gane falalar da Annabi (S.A.W.) Ya ke fadi akan Sahur, a rika daurewa ko da ruwane ana yin Sahur, idan ma ba’a sha’awar cin abinci don kar falalar ta barka dan’uwa.


FALALAR YIN SAHUR
An karbo hadisi daga  bin Malik (R.A.) Ya ce:

"تسحروا فإن في السحور بركة"

Fassara:
“Ku yi sahur domin akwai albarka a cikkin yin Sahur” – Sahih Muslim, hadisi na 2549; Ibn Majah, hadisi na 1762

Imam at-Tabari ya ruwaito hadisi cewa; Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"إن الله وملائكته يصلون على المتسحرين"

Fassara:
“Lalle Allah da Mala’ikunsa suna salati ga masu yin Sahur”

An karbo hadisi daga Amr ibn ‘Aas (R.A.); Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:

"فصل ما بين صيامنا وصيام أهل الكتاب، أكلة السحر"

Fassara:
“Babancin Azuminmu da na Yahudu da Nasara shi ne: Yin Sahur” – Sahih Muslim, hadisi na 2604; Abu Dawud, 2345; Tirmidhi, 713


__________
To be continued …. in sha Allah


29th Sha’aban, 1438 AH
(26th May, 2017 AD)


Post a Comment

0 Comments