Kamar yadda
bayanai suka gabata a rubutu na XI (Kamewa daga abubuwan da suke bata Azumi);
in sha Allah rubutun yau zai mai da hankali game da hukunci aikata wani abu da
zai iya batawa mutum Azumi, ko wanin haka.
Daga cikin
abubuwan da suke bata Azumi; akwai wadanda idan mai yin ibadar Azumi ya aikata
zai rama wannan Azuminne, akwai kuma wadanda idan ya aikata sai ya rama da
kaffara; akwai kuma wadanda aka yi rangwame akansu.
ABUBUWAN DA AKA
RANGWAME AKANSU, WADANDA BASA BATA AZUMIN MAI AZUMI
Yin Aswaki
An karbo hadisi
daga Amir bin Rabi’a Ya ce:
"رأيت النبي صلى الله عليه وسلم يستاك
وهو صائم لا أحصي أو أعد"
.
Fassara:
“Na ga Manzon Allah (S.A.W.) Yana yin aswaki a lokacin da yake yin Azumi
a lokuta da yawa, ba zan iya kirga adadin ba (da na ganshi” – Bukhari
Sumbata (Kissing)
An karbo hadisi daga Baban Hisham: Nana A’isha (R.A.) Ta ce:
"كان رسول الله صلى الله عليه وسلم ليقبل بعض أزواجه وهو صائم"…
Fassara:
“Manzon Allah
(S.A.W.) Ya kasance Yana sumbatar wasu daga cikin matansa a yayin da yake Azumi…” – Bukhari, hadisi na 1928
Jika Jiki da Ruwa Domin Jin Sanyi
Abdullahi ibn
Umar (R.A.), cikin Bukhari: باب اغتسال الصائم
"لا بأس بالمضمضة وتتبرد للصائم"
Sanya Kwalli /
Gyatima Radau / Tozali
An karbo hadisi
daga Nana A’isha (R.A.) cikin Ibn Majah hadisi na 1678 (Da’if):
"اكتحل رسول الله
صلى الله عليه وسلم وهو صائم"
Sauran Abubuwan
daka akayi rangwam akansu:
Sanya magani
ciwon idanu; da
Shafa man zoza;
da
Yin allurar
jinya marar dauke da sinadarin abinci; da
Tattaunawa yaro
da ba zai iya tauna abinci ba, da sharadin kiyaye hadiyewa; da
Dandanar abinci
ga mace mai girki dss.
ABUBUWAN DA KE BATA AZUMI WADANDA BABU RAMUWA KO KAFFARA
AKANSU
Cin Abinci ko Shan Abin Sha bisa
Mantuwa
An karbo hadisi
daga Abu Huraira (R.A.); Manzon Allah (S.A.W.):
"إذا نسي فأكل وشر فليتم صومه، فإنما أطعمه الله وسقاه"
Fassara:
“Idan (mai
Azumi) ya yi mantuwa sai ya ci (abinci) ko ya sha (abin sha) sai ya cika (karasa)
Azuminsa; Allah ne ya ciyar da shi” –
Sahih Bukhari hadisi na 1933; Ibn Majah, hadisi na 1673; Muslim, hadisi na 2716
ABUBUWAN DA KE
BATAWA DA HUKUNCIN RAMA AZUMI KADAI
Fitar Jinin
Haila, Ko Na Biki
Ga mace wacce
al’adarta ta bakunceta; kuma har ta kai ga jini ya fito ko da ko digo ne
Azuminta ya lalace zata rama Azumin wannan rana a bayan Ramadhan.
Kakaro Amai Da
Gangan
An karbo hadisi
daga Abdullahi bin Umar; Manzon Allah (S.A.W.) Ya ce:
"من ذرعه القيء، فلا قضاء عليه، ومن استقاء، فعليه
القضاء"
Fassara:
“Wanda amai (mulanko) ya rinjaye shi babu ramuwa akansa;
(amma) ga wanda ya kakaro shi (amai) da gangan akwai ramuwa akansa” - Da’ifi, Ibn Majah hadis na 1676
Kudurta Niyyar
Karya Azumi
Ga duk wanda ya
kulla a ransa cewa; shi fa karya Azumin ranar zai yi, walau ya karya ko bai
karya (ya ci abinci ko ya sha abin sha ko kuma bai ci ko ya sha) Azuminsa ya baci,
sai ya rama shi a wasu kwanaki na bayan Ramadhan (Attempt to commit an offence is an
offence).
ABUBUWAN DA KE
BATAWA DA HUKUNCIN RAMA AZUMI DA KAFFARA
Ci Ko Sha da Gangan a
Lokacin Azumi
Duk wanda ya ci
abinci ko ya sha abin sha da a zamanin kamewa kuma da gangan ba tare da wata lalura
ba, sai yayi kaffara, سنن الدارقطني hadisi na 2421:
"جاء رجل إلى النبي صلى الله عليه وسلم، فقال: أفطرت
يوماً فى رمضان متعمدًا، فقال صلى الله عليه وسلم: "أعتق رقبة، أو صم شهرين متتابعين،
أو أطعم ستين مسكينا"
Yin Jima’i da Ganga
An karbo hadisi
daga Abu Hurairah (R.A.), Imam Bukhari hadisi na 1936
بينما نحن جلوس
عند النبي صلى الله عليه وسلم، إذ جاءه رجل فقال: يا رسول الله، هلكت. قال: "ما
لك؟" قال: وقعت على امرأتي وأنا صائم. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
"هل تجد تعتقها؟" قال: لا .قال فهل تستطيع أن تصوم شهرين متتابعين؟"
قال: لا، قال: "فهل تجد إطعام ستين مسكينا؟" قال: لا، قال: فمكث النبي صلى
الله وسلم فببنا نحن على ذلك أتي النبي (ص)
بعرق فيها تمر - والعرق: المكتل - قال: "أين السائل؟" فقال: أنا، قال: "خذ
هذا فتصدق به". فقال الرجل: "على أفقر مني يا رسول الله؟ فوالله ما بين
لابتيها – يريدالحرتين أهل بيت أفقر من
أهل بيتي. فضحك النبي صلى الله عليه وسلم حتى بدت أنيابه، ثم قال: "أطعمه
أهلك"
“Wata rana muna zaune awurin Annabi (S.A.W) sai wani mutum yazo
masa ya ce: Ya Manzon Allah! Na halaka,
(Annabi) Ya ce: Me ya faru? Ya ce: Na fadawa (sadu da) mata ta alhali ina
azumi. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kana da baiwa wadda zaka ‘yanta? Ya
ce: “A’a, Ya ce: Shin kana da ikon yin azumi wata biyu jere? Ya ce: A’a, sai ya
ce: “Shin zaka iya ciyarda miskinai sittin? Ya ce: A’a, ya ce: Sai Annabi
(S.A.W) ya zauna haka bai ce komai ba. Muna cikin haka sai akazo wa Annabi
(S.A.W) awon Arak na dabino. Shi Arak wani sanho ne (ma’auni) sai (Annabi) ya
ce: “Ina mai tambaya?” ya ce: “Ga ni” ya ce: Karbi wannan kayi sadaka da shi,
sai mutumin nan ya ce: Shin akwai wanda yafini bukata kuwa? Ina rantsuwa da
Allah tun daga abin da ke tsakanin tsaunukanta biyu, yana nufin Harra biyu na
Madina, babu wasu iyalan da suka fi iyalaina bukata (talauci). Sai Annabi (S.A.W)
ya yi dariya har sai da hakoransa suka bayyana. Sa’an nan ya ce, Ka ciyarda
iyalanka da shi” – Bukhari, hadisi
na 1936
__________
To be continued
…. in sha Allah
28th
Sha’aban, 1438 AH
(25th May, 2017
AD)
0 Comments