GUZURIN
RAMADHAN XI: RUKUNIN AZUMI NA UKU (KAMEWA)
MA’ANAR KAMEWA
Kalmar ‘kamewa’
ita ce fassarar kalma Larabcin nan ta "الإمساك", ma’anarta a Shar’ance kamewa daga ci (cin abinci), sha
(duk wani abun sha), Jima’i (walau na aure ko waninsa), kame harshe (daga
karya, zance batsa, gulma, annamimanci da sauransu), da kowane irin abu ko aiki
da zai iya batawa Mai Azumi Azumi sa, daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana.
MATSAYIN KAMEWA
Kamewa dayane
daga cikin rukunan azumi uku da aka ambata a baya (Niyya, Zamani kamewa da kuma
kamewa).
HUJJAR KAMEWA
Suratul Baqarah
aya ta 187:
أُحِلَّ لَڪُمۡ
لَيۡلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآٮِٕكُمۡۚ هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمۡ وَأَنتُمۡ
لِبَاسٌ لَّهُنَّۗ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّڪُمۡ كُنتُمۡ تَخۡتَانُونَ أَنفُسَڪُمۡ فَتَابَ
عَلَيۡكُمۡ وَعَفَا عَنكُمۡۖ فَٱلۡـَٔـٰنَ بَـٰشِرُوهُنَّ وَٱبۡتَغُواْ مَا ڪَتَبَ
ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ
مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ
وَلَا تُبَـٰشِرُوهُنَّ وَأَنتُمۡ عَـٰكِفُونَ فِى ٱلۡمَسَـٰجِدِۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ
فَلَا تَقۡرَبُوهَاۗ كَذَٲلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ ءَايَـٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ
يَتَّقُونَ
Fassara:
“An
halarta a gare ku, a daren azumi, yin jima’i (saduwa) da matanku, su tufa ne a
gare ku, kuma ku tufa ne a gare su, Allah Ya sani, lallai ne ku, kun kasance
kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karbi tubarku. Kuma Ya yafe muku. To, yanzu
ku rungume su, kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. Kuma ku ci kuma ku
sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijiri. Sa’an
nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu
I’itikafi a cikin masallatai. Wadannan iyakokin Allah ne: don haka kada ku
kusance su, kamar haka ne Allah Yake
bayyana ayoyinSa ga mutane: tsammaninsu, za su yi takawa” - Suratul
Baqarah aya ta 187
Kamewa daga zantukan marasa amfani, kamar shaidar zur, zancen
batsa, karya, gulma, annamimanci, kamar yadda ya faru a lokacin Nana Maryam;
Suratul Maryam aya ta 26:
…إِنِّى نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَـٰنِ صَوۡمًا
فَلَنۡ أُڪَلِّمَ ٱلۡيَوۡمَ إِنسِيًّا
Fassara:
“…Lallai
ne, na yi alwashin azumi domin Mai rahama, saboda haka ba zan yi wa wani mutum
magana ba” - Suratul Maryam, aya ta 26
Haka nan an karbo Hadisi daga Abu Hurairah, cikin Bukhari hadisi na
1903:
"من لم يدع قول الزور والعمل به فليس لله
حاة في أن يدع طعامه وشرابه".
Sannan hatta idan wani ya zowa Mai Azumi da zancen marar amfani, ko
ya takaleshi , Manzon Allah (S.A.W.) Ya umarci Mai Azumi da ya kame, ya nisanta
kansa da fadawa musu ko zantuka barkatai kamar yadda a hadisin Bukhari, riwayar
Abu Huraira mai lamba ta 1904:
…"وإذا كان يوم صوم أحدكم فلا يرفث ولا
يصخب، فإن سابه أحد أو قاتله فليقل: إنى امرؤ صائم"
Sauran abubuwan da suke bata azumi da suka kamata Mai Azumi ya
kiyayesu; fitar da amai da gangan, fitar da maniyyi ta hanyar wasa da gaba
(azzakari) ko ta hanyar kallon sha’awa ga mace walau a zahiri, ko a bidiyo ko
ma a hoto; sanya sinadarin abinci a jiki ta hanyar allura (injection) ko
waninsa; Allah Ya bamu ikon kiyayewa
amin.
Allah ne mafi sani.
Next Eps: Abubuwan da suke bata Azumi da hukunce-hukuncesu.
___________________
To be continued …. In sha Allah
25th Sha’aban, 1438 AH
(22th May, 2017 CE)
0 Comments