Awlama (globalization)
Rashin fahimtar 'globalization' (awlama) ke sa wani lokaci ake riƙa zargin Turawa ko Yahudawa, ko 'yan film da gurɓata tarbiyyarmu.
Awlama ce ke kawo mana sabbin ɗabi'u, al'adu da tunane-tunane musamman yadda duniya ke ƙara dunƙulewa waje guda (global village). Ko ta fuskar sutura da abinci, za ka ga abincin da ake yi a Indiya, ƙasashen Larabawa, Pakistan... a yau ana yin irinsa a kan 'street' na unguwarku (shawarma, kabab, donuts...). Ka taɓa tunanin ya hakan ta faru? Mene ne ta haɗa Bahaushe da zaleka, abaya, sari, suite, jeans, t-shirt...? Ina ga yadda ake gudanar da bukukuwan aure a yau?
Ɗan Adam, mutum; da baƙar fata, da farar fata, hali ne na mutum son holewa, Ubangiji ﷻ ya ambata cikin Yusufa cewa, "ان النفس لأمارة بالسوء" sai wanda Ubangiji ya so tseratarwa, Bahaushe ba tsarkakke ne daga son holewa ba.
Idan kai da kake mahaifi, tare da mahaifiyyar yaro da kuke tare da 'ya'yanku 24/7, kuna da ikon tsawatar musu, ba su tarbiyya, sai ka riƙa zargi wai an ba wa wani kwangila su ɓata wa 'ya'yanka tarbiyya, how? Ba wani da aka ba wa kwangilar ɓatawa ɗanka tarbiyya, ka tsaya ka yi abin da ya kamata, duba da irin zamanin da kake ciki. Kana hujjar cewa kwangila aka ba wa wasu su zo su ɓata tarbiyyarka? Ko molanka ce?
Wannan ya sa Imam Ali ibn Abi Talib رضي الله عنه cikin إغاثة اللهفان mujalladi na 2 shafi na 265 yake cewa:
لا تربوا أولادكم كما رباكم أباؤكم فقد خلقوا لزمان غير زمانكم
"Kada ku yi renon 'ya'yanku kamar yadda iyayenku suka rene ku, domin an halicce su ne a wani zamani ba irin naku ba".
'Yan film, da sauran masu holewa, sabbin zubi ne na ire-iren mutanen da suke holewa a da, shekaru dubu, ko ɗaruruwan shekaru da suka gabata. Idan ma akwai masu yaɗa baɗala da iskanci a yau, ka fahimta, wasu sabbin zubi na 'yan iska ne na wannan zamanin. Kamar yadda tun kafin su Shata da Ɗan Anace akwai mawaƙa, haka su ma zamaninsu ya shuɗe, wasu suka taso da salon zamani. A da ana kiɗe-kiɗe da kalangu, ganga, goge, molo, kuntigi... a yau zamani ya zo da piano, drum set, congo... da sauran kayan zamani. Bambanci, a baya da babu media ba a ganin abubuwa a bayyane, yanzu kuma akan iya bayyana komai, abu mai kyau, da mummuna.
Globalization ne ya zo da 'NEW NORMAL', abun da idan muka gani a da (shekarun baya), sai hankalinmu ya tashi, mu ga ana yin wani baƙon al'amari, amma saboda ya zama NEW NORMAL, idan ka gani sai ka yi scrolling ka wuce. Misali, yadda ake hotunan ango da amarya, wanda ya saɓa da al'adar Bahaushe.
Ba za ka taɓa iya gyara kuskurenka ba, idan a kullum za ka riƙa zargin wasu kan matsalolinka ba tare da ka duba kanka da kanka cikin matsalar ba. Da jiya, da yau, akwai 'yan iska a cikinmu, da cikinsu. Haka nan, akwai waɗanda za su zo a gobe.
Kamar kullum ne, muna zagi da zargin 'yan film da ɓata tarbiyyar yara, amma har yau an kasa hana kallonsu, kuma sune suka fi kowa influence (tasiri) a 'media'. Su kuma sana'a suke, suna karɓar tallace-tallace da 'modelling' na kamfanoni na miliyoyin kuɗade, saboda suna da yawan mabiya, ciki har kai, da iyalanka.
Shi kuma tunani, yana shiga jikin ɗan Adam ne kamar yadda yadda abinci ke gina jiki. Tunani yana ginuwa daga abin da ake ji, gani da sauraro. Ana iya ɗaukar tunani daga karance-karance, ko kallon bidiyo ko sauraron sauti magana, ko waƙa. Irin yadda aka tsara film da ɗanka zai kalla, ya yi masa tasiri a rayuwa, kai kuma sau nawa ka sanya littafin tarbiyya kake koyawa 'ya'yanka? Wasu ɗabi'u kake nunawa naka yaran da za su tasirantu da su?
✍️ Aliyu M. Ahmad
10th Sha'aban, 1446 AH
8th February, 2025 CE
#RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad #AliMotives
0 Comments