• Ka nemi shiriyar Allah!
Don baka ƙarfin taɓewa ba kamar yadda kake wa wasu kallon taɓaɓɓu a yadda rai ke fizfizga da son aikata saɓo, "إن النفس لأمارة بالسوء".
Har na kan ji tsoro da firgici idan na ga mutanen da ake yabo a jiya sun tafka wata mummunar ɓarna, sun haɗu da wata mummunar ƙaddara, cin amana waɗanda suka amince musu, ko tafkar wani aikin alfasha... Ni da kai duk ba mu ƙarfin sauƙa a layi ba face kariyar Ubangiji ﷻ.
• Ka nemi arziƙin a wajen Allah!
Da ƙanƙan da kai da godiyar kasancewa cikin arziƙin Ubangiji ﷻ, kada ka yi fariya da kallon wasu a banzaye, marasa kataɓus a rayuwa, don kai ma ba ka fi ƙarfin karye wa ka shiga matsi da talauci kamar sauran mutane ba.
Wani ma sai a ba shi arziƙi, a haɗa shi da mummunar jinya mai naci, ko iyali, mata da 'ya'ya masu fitina su hana shi sakat.
Ba wani da abu da ka fi sauran mutane da yawonka face luɗɗufawar Ubangiji ﷻ ce. Kai kuma da ba ka da shi, ba laifin komai ka yi Ubangiji ﷻ ba, sunnar rayuwa ce ta biyo ta kanka da ƙaddara.
Be humble!
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments