Depression


Abdul 👳🏿

A lokacin da ya shafe shekara 3 yana soyayya da Ramlat, ya gama kowanne irin tanadi, ya gina gida, ya kai lefen aure da sadaki, har an saka musu ranar ɗaura aure. Kwatsam! Sai wani mai kuɗi ya fito a cikin dangin su Ramlat. Idonta ya rufe, ta yi ta shuka masa rashin mutunci. A ƙarshe, cewa aka yi Abdul ya zo ya ɗauke kayansa, saboda Ramlat ta yo sabon gamo.

A washegarin ranar da aka maida kayan lefen Abdul gidansu, mahaifiyyarsa ta rasu. An je maƙarbata janaza ɓarawo ya sace masa sabon babur da siya bayan ya yanke shinkafa. Abubuwan duniya suka taru suka yi wa Abdul yawa, ga heartbreak, ga mutuwar mahaifiyya, ga satar babur.

Abdul ya kai kusan wata guda ko fitowa ba ya yi, sai dai ya zauna a ɗaki ya yi tagumi, wani lokacin ya yi kuka. A ƙarshe dai 'depression' ya kama Abdul. Saboda ɓacin rai ma, wata rana ya fito da kayan lefen nan ya saka musu wuta a tsakar gidansu, hayaƙi da yake tashi ya sa mutane suka ankara, suka zo suka kashe wutar, aka tsince sauran kayan da suka tsira daga ƙonewa.

Ba wanda ya fahimci me Abdul ke ji a zuciyarsa, sai dai kowa ya ce:

• Abdul kai ba ka imani da ƙaddara ne,
• Abdul sai ka ce ba namiji ba,
• Abdul ni ma fa na shiga irin wannan matsalar taka, amma na daure,
• Abdul ba a kanka aka fara rasa iyaye ba,
• Abdul ba a kanka aka fara yaudara ba,
• Abdul akwai waɗanda suke cikin matsala fiye da takan nan, amma sun daure...

Ba wanda ya fahimci matsalar da Abdul yake ciki, saboda ba rauni ne a zahiri da ake gani ba. Sai da wata rana da damuwa ta yi wa Abdul yawa, ya zo fitowa daga gida ya yanke jiki ya faɗi rai ya yi halinsa (Abdul ya mutu!), sai kuma kowa jikinsa ya yi sanyi, mutane suka fara faɗi, "Allah Sarki, ya kwana biyu yana cewa ya gaji da duniyar nan".

Haka mutanenmu suke ɗaukar 'depression', shi ya sa mutane da yawa suke ɓoye damuwarsu, sai damuwa ta kashe mutum, sai a ce ya yi fuju'a. Mutane sun zaɓi su ɓoye damuwarsu saboda ba a fahimtarsu. Mun ɗauka ciwo ko rauni a zahiri jiki shi kaɗai ne jinya. Depression gaskiya ne, kuma sanadinsa na da yawa.

Wani yana da ƙoƙari a makaranta, sai ka ga GCPA nasa yana yin ƙasa, ba ka taɓa zama da shi ka tambaye shi mene ne damuwarsa ba. Wani da yake shiga cikin mutane, kwana biyu ya ɗauke kafa. Ko mai kazar-kazar a wajen aiki ya rage kwazo ko yawan mantuwa. Ko mutum ya fiye yawan ƙorafi kan wani abu na ɓacin rai... Mu kula da 'yan uwanmu, suna buƙatar kulawa ta musamman.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments