Ka Daina Damuwa Na Rashin Samun Zuwa Jami'a

Dalilin da ya sa mutanen da suka tashi cikin rashin gata, ko maraici; suka fi nasara a rayuwa shi ne; 

SUN CIRE TSAMMANIN TALLAFI DAGA KOWA, 
SUN DOGARA DA KANSU, 
DA ABIN DA UBANGIJI YA BUƊE MUSU NA FALALA.

100% na rayuwarka ya rataya a wuyanka na. Ka daina ma ɓata lokaci don jiran wani ya ba ka farin ciki, ko nasara a rayuwa.

Duk da iyaye, uncles, iyayen gida... ababen alfahari ne, ana zama wani ta sanadin wani; amma kar ka yaudari kanka da babana wane ne, uncle ɗina wane ne, ni yaron wane ne... kai kuma waye ne? Ka yi ƙoƙarin zama wani, sai ka yi alfahari.

إن الفتى من يقول ها انا ذا 
ليس الفتى من يقول كان أبي

✍️Aliyu M. Ahmad
8th Rabi'ul Awwal, 1444AH
3rd October, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments