Idan har yanzu kana jin "Bature" ko "Balarabe", ko farar fata ya fika (daraja), ko yarensu da al'adunsu sama suke da naka, tom; har yanzu kana cikin ƙangin bauta (a tunani).
Idan kana jin ƙasƙanci, saboda talauci, ko rashin kayan more rayuwa na zamani, abin hawa, ko ƙasƙanta sana'arka, ko naƙasu a halitta... kai ma kana da matsala a tunani.
Idan za ka shiga taro, kana jin kunya ko tsoron fito da wayar hannunka, saboda ta abokanka sama take da taka, ko suturarsu ta fi taka tsada... kai ma kana da "inferiority complex syndrome".
Duk sanda ka tashi auna ni'imar duniya, ka dubi na ƙasa da kai, sai ka godewa Allah; kar ka dubi na sama da kai, sai ka raina ni'imar da Ubangiji ya yi a kanka. Ka ji a ranka, kai ma mutum ne kamar kowa, iya zallar darajar ɗan Adamtaka ta isar ma tinƙaho.
Inferiority Complex 👉 https://bit.ly/3Cfixk7
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
0 Comments