Ka Kama Sana'a, Ka Daina Jiran Aiki Daga Gwamnati


Muna wani zamani da ba a jiran sai gwamnati ta ba ka aiki; kai za ka nemawa kanka mafita. 

Don ita ma gwamnatin, a yanzu; da za ta samu dama, za ta iya rage ma'aikatanta ne. Ko a baya-bayan nan, akwai wasu manyan ma'aikatu da ake shirin haɗewa, don samu rarar kuɗaɗen da FG ke kashewa.

A yau! Muna zamanin da ana karatu ne don samun saƙafa, ka ajiye kwalinka a gefe a matsayin security, ba wai don jiran aikin gwamnati ba. Idan ya zo, ka yi hamdala, idan bai zo ba, dama ka kama wasu harkokin neman na kanka.

Idan ka yi sa'a Allah Ya ba ka nasibi cikin neman halal, kai ma za ka iya zama wata ƙaramar gwamnati, har kana iya ɗaukar ma'aikata a kamfaninka, kana raba musu aiki, da albashi duk wata; tare da samun gagarumar riba.

A yau, ya kamata iyaye, da zarar yaro ya tasa, a yi ƙoƙarin kai shi wajen koyon sana'ar dogaro da kai. A baya, Bahaushe yana da irin wannan tsarin tun asali, tun kafin yaɗuwar ilimi sosai. 

Bahaushe na kai ɗansa koyon sana'a bayan an masa shayi (yana ɗan shekara 7) har ya zuwa shekaru 20 - 27 da haihuwa, duk yana wajen sana'a, don samun abin dogaro da kai (duba shafi na 22 - 23 na littafina, Wane ne Bahaushe 👉 bit.ly/3RAe7Kj).

✍️Aliyu M. Ahmad
8th Rabi'ul Awwal, 1444AH
4th October, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments