Tarbiyya Daban, Ilimi Daban


Tarbiyya daban, ilimi daban,
Ɗabi'a daban, ilimi daban.

Tarbiyya mai kyau tana koyar da mutum ɗabi'u na gari, da mu'amala mai kyau tsakaninka da sauran mutane da halittun bayan ƙasa; kamar gaskiya, amana, jajircewa, cika alƙawari, haƙuri, tausayi, kyautata mu'amala, tawadhu'u, ɗa'a da kyautatawa iyaye, girmama manya, dattako... akasin waɗannan, su ne ɗabi'u marasa kyau.

Ɗabi'a mai kyau, ba ruwanta da addini, aƙida ko wani manhaji, jahilci ko tarin ilimi, a'a; ɗabi'a tana dangantaka ga mutum (a ɗaiɗaiku; personality trait ne). Sai dai, duk mutum mai ilimi da siffar addini, ana fatan a sami ɗabi’u na gari a tattare da shi (saboda yana daga cikin abin da karanta na tarbiyyar addini).

Kada ka yi mamakin mu'amala da mutum mai tarin ilimin addini, amma idan kun zo mu'amala ya baka mamaki, ta iyu yana da ilimin ne, amma babu ɗabi'u masu kyau (musamman a ɓangaren kuɗi, amana da cika magana).

Ta iyu kuma ka samu wani nutsattse, mai ɗabi'un kirki, har kana masa kallon kamar malami, idan an zo ɓangare karatu, ka samu yana da rauni. Wani kuma, ta iyu ya haɗa duk biyun, ilimi da dabi'u masu kyau. Wani kuma ya rasa baki ɗaya. 

Abu ne mai kyau mu kula, ko wajen zaɓar abokan zama, kar ka ruɗu da iya tarin karatu kaɗai, ɗabi'a ma babbar abar dubwaa ce; za ka iya auren mace, abar kwatance a karatu, amma idan ta ma kirimɓa, ka sha mamaki, to ai ka auri mai ilimi ce, ba mai ɗabi’a ba; haka ma a cikin maza.

Idan za ka kai ɗanka ɗaukar karatu ko koyon sana’a, ka sani, zai taso da irin ɗabi’un mai ba shi horo ne, na karatu, ko sana’a; ɗabi’ar malami ma abar duba ce. 

Misali, idan ka kai ɗanka koyon sana’a ɗinki (tailoring), sai ya kasance ubangidansa ba ya cika alƙawari, ga ƙarya, zai yi matuƙar wuya idan waɗannan ɗabi'un ba su yi naso a ɗabi'un yaron ba.

Idan malamin ɗanka, wajen karatu yana yawan zafi, jifan maganganu marasa daɗi, takfiri, tabdi'i, cusa ƙiyayya, tsine-tsine, guluwi... zai yi matuƙar wahala, idan ɗalibin nan bai taso da irin wannan tarbiyyar ba, yana ɓarna, yana zaton addini yake, ai a cikin tarbiyyarsa ce. 

Duk wanda ka ga da wata ɗabi'a, mai kyau, ko akasinta; akwai wurin da ya naso ta, daga gida, wurin zama, abokai, iyayen gida, ko malamai.

✍️ Aliyu M. Ahmad
1st R/Awwal, 1444AH
27th September, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments