2013 - 2015 lokacin muna karatun Civil and Islamic Law, cikin darussan ‘Mua’amalat’, ‘Murafa’at’, ‘Fiqhul Usrat’ da Islamic Criminal Law; idan mun zo bayar da ‘reference’ daga Sheikh Yusuf Al-Qardawi, a gaban sunansa mu kan sa shekara (1926 – date), yau kuma ya koma (1926 – 2022), rayuwar ta katse, duniyar kenan!
Zai yi wuya ɗalibi mai karatun Islamic Law, ko Islamic Banking and Finance a yau, a ce bai san waye Al-Qardawi ba, da irin gudunmawar da ya bayar wajen fahimtar da fiƙhun 'jara'im wal uƙubaat', da 'masrifiyaat', 'huƙuƙ duwali', da 'maƙasid' na Shari'a, saita tunanin Musulmai a ƙarni da 20 da 21... ya tafi ya bar ilimai.
Allah Ya jiƙansa da rahama, ya amfanar da duniya da abin da ya bari na ilimi cikin rubuce-rubuce.
✍️ Aliyu M. Ahmad
29th Safar, 1444AH
26th September, 2022CE
#AliyuCares #AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
0 Comments