• Mawallafi: Prof. Ahmad Bello Dogarawa
• Yare: Hausa
• Shafuka: 179
________________________
Tarbiyya 'Ya'ya
Shekaru ko tara kuɗi, ba su kaɗai ake buƙata a wajen aure ba, ko biyan bukatarsu, a'a; ana buƙatar ma'aurata su yi karatun yadda ya kamata su tarbiyantar da 'ya'yansu, kamar yadda ba kowanne mutum ne ke iya zama malami mai koyar da ɗalibai ba, sai wanda ya yi karatu.
Rainon 'ya'ya, ba iya sama musu muhalli, abinci, sutura ba ne kaɗai ba, ko makaranta ka sa 'ya'yanka, sai dai su taya ka ba su tarbiyyar, domin haƙƙin iyaye ne. Tarbiyya ba a iya yi wa yaro wanka, da shayar da yaro ba ne.
A ƙasashe kamar Sudan, Malaysia da sauran ƙasashen Larabawa, bayan certificate na shaidar lafiya, dole ne ma'aurata su yi wani "course" na zaman aure da tarbiyyar yara kafin a ɗaura musu aure a hukumance.
Idan aka yi sa'a iyaye suka tarbiyyantar da 'ya'ya da kyau, za a yi manyan mutane, masu amfanar da al'umma, sai dai jarrabawar rayuwa. Idan aka sami akasin bayar da tarbiyya, za a sami kangararru, masu jawo wa iyayensu da al'umma fitina.
Tarbiyyar 'ya'ya abubuwa ne guda 10 kamar yadda Abu Arrad ya faɗi cikin At-Tarbiyyatul Islamiyya (p.4): Altanshi'a, Al'Islah, Atta'adib, Attahzib, Attadhir, Attazkiyyah, Atta'alim, Assiyasa, Annushu wal Irshad, da Akhlak... Farfesa yi bayaninsu daidai gwargwado.
_________________________
Za a iya sauƙe littafin (PDF) ta wannan link dake ƙasa 👇
https://bit.ly/3RzyBmX
Ko ta Telegram 👉 t.me/aliyumahmad
• Nauyi (size): 1.2MB
Allah Ya amfana.
✍️ Aliyu M. Ahmad
5th Safar, 1444AH
2nd September, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Tarbiyya #Karatu #GyaranTunani #AliyusLibrary #ReadingCulture #WeekendReading
0 Comments