#Littafi (12)
TARIHIN ANNABI ﷺ KAMMALALLE
• Mawallafi: Alhaji Abubakar Imam
• Harshe: Hausa
• Shafuka: 136
________________________
Littafin ba ya buƙatar ta'aliƙi, sai ka karanta kurum. Akwai tsakure, na tarihi da Mu'uzujin Annabawa عليهم السلام, sai tarihin Shugaba صلى الله عليه وسلام.
Alhaji ya ce:
"Ina ɗan'uwa, ga Annabawa daki-daki,
Da Allah ya zana, ko kana so ka hardace.
A Alƙur'ani za ka gan su idan ka bi,
Guda ishirin ne, sa biyar don ka ƙarasa.
Da Adamu, Idirisu, Shu'aibu, da Yasha'u,
Da Iliyasu, sa Ishaƙu, Ayuba da Salihu.
Su huɗu da Ibrahim, da Luɗu da Yunusu,
Ka sa Zakariyya, Musa da Zulƙifili, Yusufu.
Da Yahaya, da Isma'ila sa Nuhu, Haruna,
Sulaiman, sa Dawuda, ga kuma Yaƙubu.
Daɗa sai su Isah, sai Muhammad shugaba,
Da ya zo a ƙarshe don bayanin da zai gamu."
(Daga cikin littafin, shafi na 8)
_________________________
Za a iya sauƙe littafin (PDF) ta wannan link dake ƙasa 👇
Ko ta Telegram 👉 t.me/aliyumahmad
• Nauyi (size): 5.42MB
Allah Ya amfana.
✍️ Aliyu M. Ahmad
26th Safar, 1444AH
3rd September, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Tarihi #Karatu #GyaranTunani #AliyusLibrary #ReadingCulture #WeekendReading
0 Comments