Farin Jini




Farin jini jarrabawa ne, ba kamar yadda wasu iyayenmu mata ke ɗauka goshi ga ‘ya’yansu ba, har ya zama abin fariya a cikin ƙawaye. A gidan mai kishiyoyi, har habaici-habaici ake yi, da gore-gore ga wacce ƴarta ba ta da farin jini, har wasu suna neman maganin farin jini ido rufe, a wajen bokaye. 


Wasu iyayen kuma, sai su ɗorawa 'yar su maras farin jini tsangwama, saɓanin ƴar kishiyar mahaifiyarta, ko ƙanwarta, sai a maida mai farin jini ƴar lele, har ta kai ga raba zumunci tsakanin ƴaƴa. A cikin ƙawaye, sai hassada ta kunno kai, a fara ƙulle-ƙullen, da 'sihirin faraƙu', sai an raba mai farin jini da samari.


Abinda (wasu) mutanen suka gaza fahimta; farin jini daga Allah ne, jarrabawa ne, (sau da yawa) fitina ne, ga mata ko maza. Yawanci mata masu kyakkaywar sura, fuska da diri, sun fi farin jini a wajen mazaje. Idan aka yi sa’a tana da ilimi daidai gwargwado, ‘yar dangi… a idon maza wannan ta kammala, kowa zai so a ce ta zama tasa.


A cikin maza ma, a kan sami mai farin jini, duba tarihin Annabi Yusuf عليه السلام cikin Alqur’ani [Yusuf: 12: 23 - 34 & 50 - 53]. Kyan sura, kuɗi, nasaba, ilimi, addini, tsafta da kwalliya, basira, shuhura, mu’amala (haba-haba, kalamai da barkwanci),  suna daga sabubban da ke ba wa namiji farin jini a wajen mata. Wani kuma daga Allah ne. 


Mata masu farin jini ba su fiye samun kwanciyar hankali ba, abokin babanta yana sonta, cousin, abokin yayanta, malamai a makaranta, cikin dangi, cikin unguwa, ko kasuwa ta fita sai wani ya biyo ta, da mai mota da mai babur… (duk a lokaci ɗaya), mahaifiyyarta tana ta murna ‘yar ta na da farin jini, amma PSYCHOLOGICALLY, kullum ‘yar nan tana cikin tunani da zulumi (musamman kyakkyawar mace), sai ta rasa waye masoyinta na gaskiya (HUB), waye mai son ta da sharri (ISHQ; so na sha’awa).


Ga ƙalubalen hassada daga abokai, kishiyoyin uwa, dangi da mutanen unguwa, kullum cewa ake tana wulaƙanta mutane, ga barazanar mutanen banza. A ƙarshe, maza su yi ta rigima a kanta, wasu har da faɗa, wani yana mata kuka, kowa yana son sarrafa ta, ita (kuma) ta zama ‘teaser’; kuma da wuya ta auri wanda take so, sai dai wanda ya yafi farantawa iyayenta. Wata in ta shiga ɗaki, ita kaɗai za ta yi ta kuka, saboda zafin zuciya, rikicewar tunani (wannan duk iyayen ba su sani ba). Wata har ta yi aure, hatta a wajen aiki, ba za a daina bibiyarta ba.


Idan namiji ne, matan da suke bibiyarsa, wata tana ganin in ta aure shi, za ta samu kwanciyar hankali, wata kuma son sha’awa take masa, akan samu har da matan aure wani lokacin. Idan wani ya biyewa zuciya, da sunan yana da farin jini, sai ya faɗa zina, ko yaudarar ƴaƴan mutanen, saboda ana masa tallar kai da sunan so (wa’iyyazu billah). Wani har ya yi aure, mata ba za su daina bibiyarsa ba.


Idan Allah Ya jarrabe ka/ki da farin jini, kar ku yi fariya, fitinarsa ta fi yawa. Namiji ya yi koyi da Annabi Yusuf عليه السلام, tsare mutuncinka, kar a yi yaudara ko kareraya zuciyar ‘ya’yan mutane. Mace a riƙe mutunci, yaudara haramun ce, ban da rataye, a kuma dage da addu’ar neman kariya da (neman) zaɓin Allah. Idan mahaifa sun fahimci ‘ya’yansu na da farin jini, ba fariya za su yi ba, jarrabawa ce da fitina a hannunsu, su yi addu’a, su tarbiyantar da ‘ya’yansu ta fuskar rayuwa da addini.


✍️ Aliyu M. Ahmad

7th Safar, 1444AH

3rd September, 2022CE


#AliyuMAhmad

#RayuwaDaNazari

#FarinJini

Post a Comment

0 Comments