Macen da ta samu mijin aure, take shan gashi da ƙuncin rayuwa a gidan aure, ta fi ban tausayi fi ye da wacce ta jima ba ta sami mijin aure ba.
Namijin da rayuwarsa ta birkice bayan ya yi aure, ya rame, ya jeme, ya koɗe, ya rasa nutsuwa... ya fi ban tausayi fiye da wanda yake jira daga falalar Allah.
Da za mu gane wannan bambancin, da mun daina wahaltar da kanmu wajen gorantawa kowa kan maganar aure. Bal! Ka mutu ba aure, ba zai hana ka shiga aljanna ba.
Kar ka biya zuga da gori, har ka laftawa kanka kayan da ya fi ƙarfin ɗaukarka. Manufar aure, a yi, a nutsu ne, a iya sauƙe haƙƙin iyali (da kullum nauyi ƙaruwa yake, ba raguwa ba); ba a yi aure, a birkece, a shiga ƙunci ba.
✍️Aliyu M. Ahmad
6th Safar, 1444AH
3rd September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#Aure
0 Comments