Baiwa Ta Kowa Ce, Dama Ce Sai Wanda Ya Samu


Allah Ya yi mutane masu zurfin tunani da hazaƙa a cikin mutanen Arewa, masu fikiri da baiwa irin ta su Galileo, Terence, Newton, Einstein, Tesla a fasaha... 

Matsalar, idan mutum ya taso da fikira, wasu tun daga gida ake daƙushe su. Yaro zai taso da zurfin tunani, har ya iya ƙirƙirar wani abu, ya iya modelling na gini, ko mota, ko wata taswira, sai a ɗauka shirme da ɓata lokaci kawai yake na yarinta, maimakon a ƙarfafa masa gwuiwa.

Idan a wajen sana'a ne, da zarar fasaha da baiwar yaro ta fito, sai ubangida ya fara hassada, kar yaronsa ya taso ya wuce shi; daga nan sai tsangwama, da kashe gwuiwa, wani har ya ji aikin ya fita a ransa, duk da Robbert Greene a Laws of Power na cewa, "NEVER OUTSHINE THE MASTER".

Idan a makarantu ne, ba abokin gabar (wasu) malaman kamar ɗalibi mai hazaka, (wasu) gani suke kamar ya zama abokin gasa, duƙ ƙoƙarinsa sai an kai shi ƙasa. Cikin abokai ba mai ƙarfafa masa gwuiwa, sai an yi sa'a, a sami kaɗan, kamar tarihin Mark Zuckerberg da abokansa Dustin Moskovitz, Chris Hughes da Eduardo Saverin.

Baiwa 'universal' ce, ba ta taƙaita ga Turawa da sauran fafaren fata, jinsi, ko ƙabila, ko wata ƙasa ba [Al-Baqara 2:269]. Misali, abokan mahaifiyyar duk wani mai baiwa, babban fasihi, malami, ɗan kasuwa, ji suke a ransu daman ɗansu ne. Haka abokan mahaifinsa, haka abokan abokansa, ji suke, daman abokinsu ne.

Da duk mutum mai basira sai samu goyon baya, ƙarfafa gwuiwa, jagoranci (mentorship)... idan iyayensa ba su da halin ɗaukar ɗawainiyyar gina shi, community ko gwamnati ko ƙungiya su tallafa masa. Idan ya yi nasara a rayuwa, cikin rukunin mutanen da suke daƙushe baiwar mutum, iyaye, 'yan uwa, abokai, malaman makaranta, iyayen gida a wajen sana'a, sai sun fi kowa alfahari da morarsa.

✍️Aliyu M. Ahmad
6th Safar, 1444AH
3rd September, 2022

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#Baiwa

Post a Comment

0 Comments