Kalmar ‘group’ na nufin ‘rukuni’ a Hausa, ko ‘مجموعة’ (majmu’a) a Larabce. Whatsapp Group wata dama ce da Meta/Whatsapp suka bada ta haɗa mutane waje guda, don wata mu’amala ko yaɗa wata manufa da suke kai guda ɗaya.
Mutane daban-daban suna (iya) buɗe Whatsapp Group, family, classmates, ‘yan ƙungiya, shugabanni, malamai, ɗaliban ilimi, ‘yan kasuwa… kowa yana (iya) buɗe ‘group’ da wata manufa ta zumunci, ilmantarwa, sadar da saƙo, siyasa da sauransu.
Akwai wasu ƙa’idoji da ya kamata mu kiyaye wajen ta’ammuli da Whatsapp Group a matsayinmu na Musulmai, wayayyu:
1. Bai kamata ka sa mutum a group ba tare da izininsa ba.
• Akwai hatsari sanya mutum a group ba da izininsa ba, saboda, kowanne member (na cikin group) na iya shiga ya ga contacts na sauran members. Ana iya accessing na wasu bayanan sirri na mutum da lambar wayarsa. Kuma akwai doka ta ‘data protection’ a sashe na 37 na Constitution (CFRN 1999) [bit.ly/3Jtfxns] da NDPR (bit.ly/3QhzL5I) kan hakan.
• Yawancin waɗanda ake yiwa ‘hacking’ na Whatsapp, a group(s) ake ɗaukar lambobin wayarsu.
• Akwai wasu mutanen da ake ƙira da SERIAL SETTER-UPPERS, halinsu duk sanda wani abu ya faru, sai sun buɗe group sun sa mutane. Misali: Happy Sallah Group, New Year Group, Ramadan Group… da sauransu.STRAIGHT OUTTA, su ne duk group ɗin da ka sa su (adding), za su fice. Group ko na addini, akwai buƙatar neman izinin mutum, kafin ka sa shi.
• Za ka iya dakatar da sanya ka cikin Whatsapp groups har sai (in) ka so. Ka shiga Setting > Account > Privacy > Groups > My Contacts/MyContacts Except (sai ka selecting duk contacts). Ba wanda zai sa ka a group (kai tsaye), sai dai ya turo ma link, in ka ga dama ka shiga, in ka ga dama, ka ƙi shiga.
2. Turo abin da baya daga cikin manufofin group:
Wasu NA TURO ABIN DA BAI SHAFI MANUFAR BUƊE GROUP ba. A cikin hadisi, Annabi ﷺ Yake cewa: «المسلمون عند شروطهم إلا شرطًا حَرَّمَ حلالًا أو شرطًا أَحَلَّ حرامًا .» Ma’ana, “Musulmai suna kan sharuɗɗansu (ba za su saɓa ba), sai dai in sharaɗin na haramta halal ne, ko na halarta haram.” (Bukhari, 2721 & Muslim, 1418).
• Idan group na family ne, iya abun da ya shafi family ya kamata a sa a group, in na ilimi, a sa abin ilimi kaɗai, in na sadarwa ne ma, haka. Bai kamata ka sa abin siyasa a group da ba na siyasa ba, matuƙar ka san akwai wanda ba wannan ra’ayin yake ba, haka turo talla da yawa da sauransu.
• Idan akwai yaren da ake magana da shi a group (lingua franca) mis. Larabci ko Turanci ne, bai kamata ka sauya yare ba, saboda waɗanda ba sa jin naka yaren, za su zaton kana gulmarsu ne. Manzon Allah ﷺ Ya yi hanin juya magana cikin mutane, har su ji kamar kana yi da su ne (Bukhari, 6290).
• Idan cikin group da yake akwai waɗanda ba Musulmai ba, kuma an ƙirƙiri group da (wata) manufa da ba ta sanya wani abun addini ba, bai kamata kai ka sa abin addini ba, saboda saɓa ka’ida ne (a cikin wancan hadisin na sama), zai iya kawo tashin hankali. Misalin hatsarin irin wannan, abin da ya faru a Sokoto ranar 12 May 2022 (bai kamata ka yi aikin da za a taɓa mutuncin addininka ba).
3. Idan cikin group ɗinku da mata, bai kamata ka zage kana ɗaukar ‘contacts’ ɗinsu ba, kana bin su ta DM/PM kana: hello, hi, ykk… wannan ko ba marji’i na ilimi, kai ma ba za ka so a bi matarka, ƙanwarka, ko ‘yarka ta private ana mata magana ba.
4. Idan abu da bai fashe ka, ka kame daga shiga don gudun ƙara fitina. A cikin hadisi, Annabi ﷺ Yake cewa: “من حسن إسلام المرء تركه ما لا يعنيه” Ma’ana, “Yana daga cikin kyawawan ɗabi’un Musulmi, ya bar abin da babu ruwansa” [Tirmidhi, 2317].
5. Ka gujewa halin SHARER, sune masu halin ‘everything should be forwarded” komai suka samu, sai sun muku forwarding cikin group, su cika group da messages. Mu sani, mutane suna da wasu groups ɗin, suna (kuma) da sauran harkoki, ya kamata ana limiting (iyaka) na turo 'messages' a cikin groups. Buƙatar duk wanda ya turo saƙo, a duba, mene ne amfani turo abin da ba a dubawa?
6. Ka guji shiga groups da ake yaɗa alfasha da batsa, yin gulmar mutane, annamimanci, Malam Mai Alkhadary na cewa: “ لا يحل له صحبة فاسق ولا مجالسته لغير ضرورة…” Ma’ana “baya halatta (ga Musulmi) ya zauna da fasiƙi, sai in da lurara ta dole-dolen”. Akwai kuma aya cikin An-Nisa’i 4:140. DUK ABIN DA AKE NA SAƁO A WHATSAPP, DAIDAI YAKE DA ABIN DA AKE A RAYUWAR ZAHIRIN. A Whatsapp group kam in ka ga alfasha ta yi yawa, kana da ikon ficewa daga group. Leave!
7. Duk abin da ka yaɗa na alheri ko sharri kana da kamasho. Abin alheri sadaka jariya ne gareka, har izuwa ranar tashin Alƙiyama [Sunan an-Nasa'i, 3651].
Annabi ﷺ Yana cewa: “من علَّم علمًا فله أجرُ من عمِل به ، لا ينقصُ من أجرِ العاملِ” Ma’ana: “Duk wanda ya sanar da wani ilimi, yana da ladan (irin) na wanda ya yi aiki da shi, ba tare an tauye daga ladan wancan da komai ba” [Ibn Majah, 246 ].
✍️Aliyu M. Ahmad
6th Muharram, 1443AH
4th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Whatsapp #WhatsappGroup #BeCyberSmart
0 Comments