Har yanzu muna raina MEDIA ko? Muna ɗaukar media a iya wurin a yi nishaɗi, a yi raha a yi chatting, a tallata kaya... kawai!
To:
MEDIA MAKAMI CE!
MEDIA NA'URAR JUYA TUNANI CE!
Ba mu san cewa media komai da komai ba ce, yanzu ga shi yaƙi yana cimmu, ana haɗa mu gaba da faɗa tsakaninmu...
Ba ka san wannan #saga ta HAUSA/FULANI kintsa ta aka yi ba? Kuma an yi nasara, tunda har masu ganin kansu a masu ilimi ma sun shiga faɗan.
Ana amfani da ilimomin PSYCHOLOGY, da MOTIVES dinmu, ana amfani da LEVEL OF TOLERANCE da muke da shi, ana tuso mana wasu tunane-tunane, ga PSY OPS, FALSE FLAG, CONSPIRACIES, ga PROPAGANDAS...
Idan ba mu tashi tsaye ba, mun yi wa kanmu Ƙiyamul Lail, wallahi 'ya'yanmu da jikokinmu ne abin tausayi, yanzu ma sai abin da aka ba mu muke karɓa a media, ana MANIPULATION mu, ina ga next generation? Tunda mun taƙaita media a wajen nishaɗi?
Gaskiyar Na'ibi Sulaiman Wali: "ABIN DAKE BAMBANTA MUTUM DA DABBA TUNANI NE. BA A YIN TUNANI MAI ƁULLEWA SAI DA ILIMI. ILIMI KALA 2 NE, AKWAI NA LAHIRA (ADDINI) DA NA DUNIYA (ZAMANI). IDAN KA KEƁANTA DA ƊAYA, KA JAHILCI ƊAYA, ZA KA FAƊA TARKON ƊAYA KA HALAKA." (Daga: النور الدلال فى ترشيد الأطفال، p. 6 - 7: The quotation has been edited).
Ilimi ba ƙarya ba ne! Matuƙar za mu jahilci nazari game da me duniyarmu ke ciki, tabbas za a yi ta haɗa ma sharri, da tuggu, da ilmomin da muka jahilta, ba sai an kashe mu da bingida ba, mu za mu kashe kanmu da kanmu, ana haɗa mu faɗa. Tunani kuma, sai wanda aka so mu yi, za mu yi.
Me ya faru kafin yaƙin ƙare dangi na Rwanda (na Hutu, Tutsi da Twa, 1994)? MEDIA.
Me ya taimaka sosai wajen jan hankalin duniya kan #ENDSars? MEDIA
• Idan ka hau kan internet, kana neman bayani game da kanka, ba kai ka rubuta ba, su suka rubuta.
• Mene ne tarihinka? Su suka rubuta.
• A wacce irin ƙasa kake zaune? Ya za ka tsara yadda za ka bautawa Ubangijinka a ƙasar ba tare da kaucewa dokokin Sharia ba? Ba mu sani ba.
• Manyan gidajen jaridu na su ne, sai abin da suke son mu ji, za mu ji. Kuma su suke bayyanawa duniya MU, da ƙasarmu. Muna raina aikin jarida ko?
• Yadda muke a idon waɗanda ba Musulmai ba, daban, da yadda muke a zahirinmu. Rubutunsu ne, kuma shi ne a yanar gizo.
Allah Ya jikan Sheikh Abubakar Gumi, da ya faɗi wata magana akan siyasa, an masa mummunar fassara, ga shi nan, muna ibada cikin ƙunci da taƙaici, da matsi; muna tafiye-tafiye cikin fargaba da tsoro... saboda siyasar ƙasar ta kasa tsinana mana komai.
Ka karanta:
MEDIA MANIPULATION AND PSYCHOLOGICAL WAR na Vladislav Saran: bit.ly/3P3jU9Q
THE MEDIA AND THE RWANDA GENOCIDE na Kofi Anan: bit.ly/3SpHrVr
VOICES OF WAR: CONFLICT AND THE ROLE OF THE MEDIA na Andrew Puddephatt: bit.ly/3bpWWw4
WAR AND MEDIA na William E. Biernatzki: bit.ly/3SsrrSo
✍️Aliyu M. Ahmad
6th Muharram, 1443AH
4th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Siyasa #Media
0 Comments