A kowanne matakin rayuwa akwai ƙalubale, amma idan kana neman rangwame cikin kowanne ƙalubale, sai ka shirya taryarsa tun kafin ya ƙaraso.
Sau da yawa in an tambayi undergraduate, YAUSHE ZA KA YI AURE? "ai sai na gama makaranta..." amsar kenan. Sai ka gama makaranta immediately kana karɓar kwalinka za ka yi aure? To ai bayan ka karɓi kwalin ma, kana buƙatar aiki ko? Kai! Kafin ka sami aiki sai ka tafi NYSC...
Aure nufi ne na Ubangiji, amma a fahimtata idan kana da sana'a, after graduation kana nufin, a lokacin hankalinka ya dawo waje ɗaya ne. Amma yawancin matasa masu lissafin, AFTER GRADUATION, tunanin aiki ne.
Rayuwa kowa da yadda Allah Ya tsara masa. #AfterGraduatiom, wani dama tuntuni yana da sana'a ko aiki, wani kuma tun kafin ya tafi NYSC zai sami aiki, wani yana cikin yi service zai sami aiki, wani yana kammala NYSC zai samu aiki da wuri, wani kuma sai ya jira shekaru... mafi dahir shi ne wanda ya fara taimakon kansa, ya nemi sana'a kafin Allah Ya kawo masa aikin da yake mafarki.
Mu je lissafi:
NYSC shekara ɗaya ne (sati 3 a camp, wata 11 a service), za a riƙa baka ₦33k alawus a wata, ₦33,000 x 11 = ₦363,000. Tambayar a nan ita ce, ₦363k ta isa ta ma aure? Dakata, ba ma za ka iya tara wannan kuɗin ba (₦363k), saboda a kowanne wata, akwai expenses, feeding, recharge card, sabulun wanka da wanki, transport..., a ka tsira, ka tsira da ₦10k zuwa ƙarshen wata, ₦10k x 11months = ₦110,000 (wannan ya isa aure?) a'a. Daga nan za ka fara lissafin samun aiki.
Mu yi lissafin a labour market:
Ƙaddara kana kammala NYSC ka samu aiki da wuri, da digiri. Albashinka da alawus-alawus, yawanci graduate na samun aiki a GL07 ₦75+ ne a wata (koyarwa, aikin tsaro ko na office a matakin jiha). Ma'aikatan lafiya kuma a kan CONHESS 07 ₦80k+. Lecturing, Assistant Graduate ke kaiwa ₦90k+, sai masu aiki da federal agencies (aikin mai tsananin rabo), FMC, CBN, NIMASA, NNPC, BOI... da ke ɗaukar mai tsoka shi ma ya danganta da wurin aiki (alawus) a ma'aunin NSIWC.gov.ng.
Aiki da private organization kuma ya danganta da shirin (project), aikin (assignment) da kuma wurin da za a yi aiki (location). Misali, mai aikin banki a wani wajen ana iya samun ₦100k+, ₦250k+... ya danganta da banki ko aikin. Haka NGOs, musamman na harkokin lafiya.
Idan kuma private school za ka koyar, mafiya yawanci, masu samun da yawa ₦20k - ₦35k ne (graduate), a wasu wuraren ma, har da masu ₦10k, ₦15k... a wata. Haka ma aikin gidan radio, ko private hospital (na rufin asiri ne).
Mu dawo lissafi:
Mu ɗauki misali, ka sami aikin da ake biyanka ₦100k a wata, a shekara 'annual earning' ₦1.2m kenan. Amma ₦1.2 za ta ma aure? Kuma fa kar ka manta, sai da ka yi service 1yr, ka fara aiki 1yr, shekara 2 kenan AFTER GRADUATION.
Akan wannan ₦1.2m ɗin dai, a duk wata in ka samu ₦100k, ba tarawa za ka na yi ba, a'a, akwai buƙatun yau da gobe (abinci, sabulun wanka da wanki, magani, zirga-zirga, alheri wa iyaye, 'yan uwa da abokan arziki da sauran nauye-nauye). A ka tsira da wani abu, a je ₦50k, misali. ₦50k x 12 (shekara) = ₦600k. ₦600k za ta ma aure?
Kar ka manta, kana buƙatar mallakar gida (ko da na haya ne), idan ginawa za ka yi, a ƙalla ka kashe 2m - 3m, gidan haya kuwa mai kyau zai kai ₦100k duk shekara. Akwai kayan al'ada, zai lamushe ma kusan ₦750k+, kyautawar soyayya, da sauran nauye-nauye da shirye-shirye... a ƙalla kafin ka kawo mace gidanka ₦3m sai ta ɓace (har ginin gida). Tsawon wane lokaci za ka ɗauka kafin samu waɗannan kudaden?
TAMBIHI
1. SANA'A ITA CE DAHIR! Hanya mafi ɓullewa a yau, ka nemi sana'a, ita za ta rufa ma asiri. Ka koyi wani skill, ga su nan baja-baja. Idan ka lura da kyau, YAWANCIN ABOKANKA na primary da secondary da suka yi aure, ba su je jami'a ba, ba kuma aikin gwamnati suke ba, sana'a ko kasuwanci suke.
2. Kar tada kanka hankali, kar ka matsawa kanka, ka bi komai a sannu, aure da mutuwa, komai lokaci ne, wanda bai kai shekaru ba ma ya mutu, amma har yanzu ga ka a raye.
3. Ga wasu rubututtuka masu alaka:
• Yaushe za ka yi aure 👉 bit.ly/3SbtXN3, bit.ly/3vuAXL4
• Matasan zamani da soyayya 👉 bit.ly/3zoJwIz
• Jinkirin aure 👉 bit.ly/3Q2dhFW
Allah Shi ke tsara rayuwa, amma idan ka yi iya naka ƙoƙari, zai Allah Ya taimake ka.
✍️ Aliyu M. Ahmad
3rd Muharram, 1444AH
1st August, 2022CE
#AliyuMAhmad #AliyuCares #RayuwaDaNazari #Aure #iThink #MarriageAfterGraduation
Photo Credit: Arewa Fashion Style
0 Comments