Nijeriya



A fiqhun Huquq al Duwaliya, Nijeriya ba Daulah Islamiyyah (Islamic State/دولة إسلامية) ko Daulah Muslimah (Muslim State) ba ce, Secular State ce. Kuma dama can Sharia ta tsara mana yadda za mu yi rayuwa, a kowacce ƙasa muka tsinci kanmu (a matsayin Musulmai), har a ƙasar abokan gaba ( دار الحرب) ko wacce ake sulhu (دار العهد/دار الصلح) da sauran tsare-tsaren diflomasiyya.

Daulah Islamiyya (Islamic State) ita ce ƙasar da 'yan ƙasar Musulmai ne, kuma an gina ta tare da tafikar da lamuranta bisa tsarin Shari'ar Musulunci (الإسلاموية). Misali, Saudi Arabia. A da can an taɓa Daulolin Musulunci da suka mamaye wasu yankunan Nijeriya, da Afrika;.mis. Daular Sokoto (1804 - 1903), da Kanem–Bornu (700 - 1893), a 1900s zuwan Turawan Mulkin Mallaka, suka maida daulolin ƙarƙashin sabon tsari. Sarakunan suna nan, amma tsarin na Sakulanci ne.

Akwai ƙasar da Musulmai sun fi yawa, amma tsarin gudanawarsu ba na Musulunci (Shariah) ba ne, misali Niger (kasar Nijar) 99.3% na 'yan ƙasar Musulmai ne.

Shi kuma tsarin SAKULANCI, an gina shi bisa tsarin raba addini da harkokin gudanarwa, amma yana ba wa 'yan kasar damar rayuwa bisa wani addini, ko tunani (mis. sashe na 38(1) CFRN), sannan kar gudanarwar addini ta ci karo da dokokin ƙasa (mis. section 1(1) CFRN).

Tsarin siyasar Nijeriya ba na Shariah ba ne, dimokradiyya ne, yana tabbatar wa da ƴan ƙasa ƴanci na Fundamental Human Rights a cikin Chapter 4 na Constitution tare da bawa 'yan kasa damar zaɓar wakilai da za su tsara musu dokokin gudanarwa. Bayan CFRN (1999), akwai sauran kundayen dokoki (acts, laws da bye-laws) da suke gudanar da sauran al'amuran ƙasa.

'Yan Nigeria 53.5% ne Musulmai, 45.9% Kiristoci ne, sauran 0.6% ne na masu addinin gargajiya, Yahudawa da Maguzawa (CIA World Fact, 2019). Fanaticism ne don kana zaune a Arewa, kana tunani, Nigeria duk ta Musulmai ce (kaɗai), ko ƙasar Musulunci ce, haka ma wanda ake zaune a lungun Obatebe, yake tunanin Nijeriya ta Kiristoci ce. Kamar haka wani can da yake cikin wani loko a Indiya yake tunanin, duk duniya addinin Hindu ake yi, ko wani can da yake rayuwa a dutsen Alantika, yana tunanin, duk 'yan Nijeriya maguzawa ne, da ganye suke suturta al'aura.

'Yan siyasa na amfani da farfagandar siyasa da sunan addini ne a lokacin zabe, amma bayan zabe, ba ruwansu da addini. Ba da Alkur'ani ko Bible ake gudanar da mulki ba, da Constitution ne (ka zaɓi wanda zai zame ma maslaha a rayuwar duniya da lahira, ko ba Musulmi ba ne). An bawa Shariah dama ne kaɗai a harkokin da suka shafi m'amala, aure da rabon gado... sune tsarin shari'arsu (murafa'at/procedure) irin na Musulunci ne, bisa fiqhu Malikiyya. Mis. ana yawan amfani da Jagoran Masu Hukunci (Tuhfatul Hukkam) na Al-Garnadi a Sharia Courts.

Kuma yana da kyau a ƙalla kana dan Nijeriya, wayayye, bayan ka karanta fiqhun Shariah, ka kuma karanta fiqhun dokokin Nijeriya, don kada a ruɗar da kai domin kuɓuta daga kangin bautar tunani. Shi ya sa mai littafin النور الدلال Na'ibi Sulaiman Wali yake cewa:

العلم دنيوى وأخروى كل مطلوب منك. فإيك والاقتصار على أحدهما فتغرق فىشر الآخر. فمثالهما لك كمثمل الطير له الأخروى، فإذا اجتهد فى هذين العلمين هديت بالهداية، وإلا بليت بالغواية.

"Ilimin zaman duniya da na neman lahira dukkanin ababen nema ne, idan kuma ka taƙaita da guda ɗaya, za ka nutse a sharrin ɗaya, saboda dukkan biyun, kamar tsuntsu ne mai fukafukai guda 2, idan ka dage akan neman sanin waɗannan ilimai guda biyun, za ka sami shiriya, idan ba haka ba, za ka gamu da fitina" [النور الدلال فى ترشيد الأطفال، p. 6 - 7].

Ka karanta fiqhun Constitution, The Nigerian Constitutional Law (2006) na Ese Malami, ka nemi sanin dokokin da Nijeriya ta tanada na abin da ya shafe ka, dokokin hanya (FRSC Act 2007), amfani da ƙasa (Land Use Act 1978), mu'amalar kasuwanci (CAMA, NIPC...), zaɓe (Electoral Act 2022),... Ka duba littafin At-Tibyan, The Doubt Regarding the Ruling of Democracy in Islam (bit.ly/3cWMFYg), ka duba littafan Musulunci a kan tsarin siyasa mulukiyyah, sultaniyyah, da diflomasiyya na malaman Musulunci irin su Ibn Taymiyyah, Maududi, Imamul Ghazali, Mawardi... رحمهم الله.

Idan ka ce, ai idan mutum ya yi laifi ma a Nijeriya, ba da Alkur'ani ake masa hukunci ba, akwai kuma aya ta 44, 45 da 47 cikin Ma'ida (ومن لم يحكم بما انزل الله...), to kai me ya kai ga aikata laifi da har za a ma Shariah da ba ta Allah ba? Sata, kisan kai, tsafi, ƙazafi, cin amana... duk laifi ne, a Shariah da kuma cikin Penal da Criminal Codes.

✍️Aliyu M. Ahmad
2nd Muharram, 1443AH
31st July, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Siyasa

Post a Comment

0 Comments