Marka-Marka I


Idan za a yini ana ruwan sama, to kai ma sai dai ka yini kana zaune cikin ɗaki kai kaɗai, kana ta latsa waya 😔🤳 


In kai ba 'Mama's boy, ba ne, ka zauna kana ta hammar yunwa... In baka da mota, kana tsoron fita. Ina babu wutar lantarki, caji ya ƙare ma, waya ta rufe... sai kuma ka buɗe tunane-tunanen duniya... ka ƙulla, ka kwance...


Amma idan kana da iyali kuwa:


1. Ba zance tunanin yunwa ma (matuƙar akwai abin da za a sarrafa a gida). Maras aure kam, sai neman gafarar Allah, a yi ta Istigfari...📿 


2. Ba buƙatar sai ka fita, ka shiga cakwaɓi, ladan na صلوا في رحالكم za ka ja iyalanka sallar Jam'i. Kai ko ɗan uwana, sai dai ka yi kayarka, kai kaɗanka, murfadi.


3. Kana cikin karatu, za a leƙo a ce ma, "sannu babban baby". Kai ko ɗan uwana, sai in MTN sun iyo ma text, zaka duba da sauri, kana zaton Bank Alert ne, sai ka ga #MoMoPSB.


4. Idan kana da ƙaramin yaro/yarinya, ka ɗauka kana ririta abinka, kuna wasa; idan ko kai ma ɗan uwana ne, sai dai ka dinga canjawa pillow guri/wuri, daga saman gado, zuwa kan seater, can kuma kan floor...


A kowanne yanayi, AURE RUFIN ASIRI NE.  Wannan duk kaɗan ne daga cikin rufin asiri da falalar aure, ta fuskar addini, al'ada, zamantakewa, halayya, tattali...


Allah Ya azurta mu daga falalarsa 🤲


✍️ Aliyu M. Ahmad 

18th Dhul-Hijjah, 1443AH

17th July, 2022CE


#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Aure

Post a Comment

0 Comments