Kana Mamakin Ana Samun Wasu Marasa Kunya a Tiktok ko?

 



Kana mamakin ana samun wasu marasa kunya a Tiktok ko?


Wataƙila in ka shiga TIKTOK ka tarar da wasu mata na zage-zagen junansu, tonan asiri, habaici da sauransu... Idan ka ji wata tana zagin waccar, za ka so ka ji me ya haɗa su. Sai ka je ka buɗe bidiyon abokiyar faɗan nata (ka buɗe x2 kenan).


MALAM JI NI! Duk ENGINEERING ne, da kansu suke ƙirƙirar hakan, domin mutane su je TSURKU, ba wani SAƁANI A TSAKANINSU... don su sami traffic (adadin masu buɗe videos nasu) ne, daga nan, TIKTOK ya fara biyansu da miliyoyi, kun taimaka musu kenan.


Idan mutanen ƙirƙi ba su yi amfani da wannan damar ba, mutanen banza za su kwashe moriyar da ake samu a social media. 


Shi ya sa, ni bana ganin cewa RIYA ce, don wani ya zo SOCIAL MEDIA yana karatun Alƙur'ani Maigirma. NIYYA A ZUCIYA TAKE. Mutanen banza ma na yaɗa barna, kuma ana gani.


Da zarar wani ya ta so da niyyar fara yaɗa baiwar QIRA (ta karatun Alƙur'ani Mai girma), sai a kashe masa gwuiwa, ana faɗin RIYA CE, RIYA CE... ka duba Channels na ISLAM SOBHI a Youtube (www.youtube.com/c/islam_sobhi) 4.54M subscribers, millions of viewers, kasan adadin miliyoyin da SOBHI ke samu? Kai ka ce, mu kaɗai ne Hausawa muke abu don RIYA (yi ba don Allah ba). 


Idan ana maganar a yaɗa BAIWA da BASIRA a social media, bana tunanin akwai baiwar ta kai ta ALƘUR'ANI MAI GIRMA a wajenmu Musulmi.  In ba a yaɗa alheri ba, masu yaɗa sharri kullum ƙaruwa suke a media. Kuma suna amfani da sharrin, suna samun kudi. Na ga wani ma (Mai Wushirya) har Umrar bana ya je, kuma bana zaton ba TIKTOK ne sila ba.


Babu wata manhaja da ba za a iya yaɗa SHARRI ko ALHERI  a cikinta ba, wannan yana da NASABA da mu ne, masu amfani da dandalin.


MU SAKE TUNANI!


Allah Shi ne mafi sanin daidai.

Allah Ya sa mu da ce.


✍️Aliyu M. Ahmad

17th Dhul-Hijjah, 1443AH

16th July, 2022CE


#AliyuMAhmad #FasaharZamani #Tiktok #RayuwaDaNazari #SocialMedia #MuSakeTunani

Post a Comment

0 Comments